Hotunan tsoho mai shekaru 88 ya kammala digiri rana daya da jikarsa mai shekaru 23
- Wani tsoho duk da cikarsa shekarunsa 88 da kuma rashin kuzari a jikinsa, ya samu nasarar kammala digiri a jami’a
- Ya yi digirin ne a fannin tsumi da tattali kuma ya kammala a rana daya da jikarsa mai shekaru 23 ta kammala digirin ta
- Rene Neira ya samu nasarar cika burinsa na aiki a banki wanda dama tuntuni yake da kudirin karatu a fannin tattalin
Ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare. Wani tsoho mai shekaru 88 ya tabbatar da wannan karin maganar bayan cika burinsa wanda ya dauki tsawon lokaci a zuciyarsa.
Ya samu nasarar kammala digirinsa a jami’ar Texas da ke San Antonio inda ya yi karatu a fannin tattali.
Abinda zai kara burge mai karatu akan labarinsa shi ne yadda ya kammala digirin tare da jikarsa, Melanie Salazar.
Ya dade ya na da burin karatu a fannin tattali na kudancin San Antonio. A shekarar 1960 ya dinga gwagwarmaya hakan bai ba shi damar komawa makaranta ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Tun bayan lokacin ya ke da kudirin karatu a fannin tattali, Today ta ruwaito.
“Abin da dadi kasancewar ni da kakana duk mu na jami’a guda, amma sai na zo na saba ma,” a cewar jikarsa.
Yanzu haka mutumin ya kammala digirinsa a fannin tattali wanda hakan ne cikar burinsa.
Melanie ta sanar da today.com cewa abin ya bayar da mamaki saboda yanayin jikinsa don ba shi da lafiya isassa.
“Na yi matukar jin dadin yadda UTSA ta ba shi dama har ya iya kammalawa, har kula da shi aka yi saboda jajircewarsa,” inji jikarsa.
Mutumin da aka kora daga makaranta ya mallaki N32trn, ya zama mafi arziki a China
A wani labari na daban, idan daukaka ta zo wa mutum, kowanne irin aiki ko sana’a ya je yi sai ya bunkasa fiye da tunanin jama’a.
Sana’ar ruwan gora Zhong Shanshan ya fara, yanzu haka ya zama mutum mafi dukiya a kasar China inda ya ke da Naira tiriliyan 32.1 daidai da dala biliyan 77.4 inda mai Alibaba, Jack Ma ya koma kasan sa inda ya ke da Naira tiriliyan 16.06 daidai da dala biliyan 38.7.
Kididdigar Bloomberg’s Billionaires ta gano cewa dukiyar Shanshan ta zarce naira tiriliyan 40. Shanshan ne mai ruwan gorar Nongfy Spring da kuma Wantai Biological Pharmacy Enterprise a Shanghai.
Asali: Legit.ng