Tsohon shugaban kasar Gambia zai fuskanci fushin doka saboda kashe wasu 'yan Najeriya
- An ta'allaka wasu munanan kashe-kashe na kiyashi a kan tsohon shugaban Gambia, Yahya Jammeh, ciki har da na 'yan Najeriya
- Kwamitin bincike na kasar da shugaba Adama Barrow ya kafa ya bayyana cewa Jammeh ya bada umarnin kashe wasu bakin haure 'yan Afrika
- Daga cikin wadanda mabiya tsohon shugaban suka kashe har da wasu daga yankin yammacin nahiyar Afirka, wadanda wasu daga cikinsu ‘yan Najeriya ne
Kwamitin gaskiya, sasantawa da ramuwa ta Gambia (TRRC) da shugaban kasa Adama Barrow ya kafa a shekarar 2017 ta bayyana cewa tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh ne ke da alhakin kashe wasu bakin haure 'yan Najeriya da wasu 'yan Afirka da dama.
A wani rahoto da hukumar ta fitar a baya-bayan nan, ta yi ikirarin cewa manyan hafsoshin sojan Jammeh ne suka tsare bakin haure ‘yan Najeriya wadanda daga baya aka yi musu kisan gilla, inji rahoton The Nation.
TRRC ta bayyana cewa jami'an na Junglers (kamar yadda ake kiransu) sun samu umarni ne daga Jammeh yayin da yake kan mulki kafin saukarsa a shekarar 2017, in ji Vanguard.
Hukumar ta ce tsohon shugaban kasar tare da wasu za a gurfanar da su gaban kuliya bisa laifin cin zarafin bil adama.
Wannan kenan baya ga zargin cewa Jammeh na da laifin cin zarafi da kame 'yan jaridun Gambia ba bisa ka'ida ba, da kisan 'yan kasar 17, a cikin wasu munanan ayyukan na zalunci inji rahoton.
An gurfanar da wata mata a kotu kan 'cin zarafin' sufetan 'yan sanda a Legas
A wani labarin na daban a Najeriya kuwa, 'yan sanda sun gurfanar da wata mata gaban Kotun Majistare da ke Badagry a Jihar Legas bayan cin zarafin sifetan ‘yan sanda, Punch ta ruwaito.
Wacce ake karar ta na fuskantar laifuka biyu ne, daya na cin zarafi sai kuma tayar da zaune tsaye.
Mai gabatar da kara, ASP Clement Okuiomose ya sanar da kotu cewa wacce ake zargin ta aikata laifin ne a ranar 8 ga watan Disamba da misalin karfe 10 na safe a haraban kotun majistaren da ke Badagry a jihar Legas.
A cewarsa ta ci zarafin sifeta Modinat Esho wacce ma’aikaciya mai lamba 234392 da ke aiki da kotun majistare ta uku a Badagry, ta hanyar hankada ta kasa yayin da ta ke kan aiki. Okuiomose ya ce wacce ake kara ta tayar da tarzoma ta hanyar hankada mai kara.
Asali: Legit.ng