An rufe masallaci a Faransa saboda huɗubar tunzura jama'a

An rufe masallaci a Faransa saboda huɗubar tunzura jama'a

  • Mahukunta a kasar Faransa za su rufe masallaci a kasar saboda wa'azin tunzura al'umma da ake zargin limami da yi
  • Gwamnatin ta ce limamin masallacin ya mayar da hankalinsa ne wurin yin wa'azi da ya shafi kiristoci, yahudawa da masu auren jinsi
  • Tuni dai an fara gudanar da bincike tare da tattara bayanai yayin da za a rufe masallacin tsawon watanni shida

Gwamnatin Faransa ta bada umurnin a rufe wani masallaci a arewacin kasar saboda abin da ta kira hudubar tunzura jama'a da limamin ke yi, Sahara Reporters ta ruwaito.

A wani rahoton AFP, za a rufe masalllacin da ke Beauvais na tsawon wata shida a cewar mahukunta na yankin Oise inda Beauvais.

An rufe masallaci a Faransa saboda huɗubar tunzura jama'a
Faransa za ta rufe masallaci domin hudubar tunzura al'umma. Hoto: REUTERS/Christian Hartmann
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Buhari zai iya kawo karshen ta'addanci kafin cikar wa'adin mulkinsa, Femi Adesina

Mahukuntan sun yi ikirarin cewa wa'azin da ake a masallacin na koyar da kiyaya, tashin hankali da 'kare jihadi.'

Hakan na zuwa ne makonni biyu bayan Ministan Harkokin Cikin Gida, Gerald Darmanin, ya ce ya fara shirin rufe masallacin domin limamin yana koyar da kiyaya ga 'kirista, masu auren jinsi da yahudawa' a wa'azinsa.

Wannan, Ministan ya ce, ba za a amince ba.

A cewar rahotanni, kamata ya yi mahukuntan yankin su shafe kwana 10 suna tattara bayanai kafin daukan mataki amma, yanzu, za a rufe masallacin cikin kwana biyu.

Bayan rayuwa cikin daji yana cin ciyawa, yanzu wankan sutturu na alfarma ya ke yi, ana girmama shi a gari

A wani rahoton, wani matashi, Nsanzimana Elie ya kasance a baya ya na zama cikin daji saboda yanayin suffar sa, sannan mutanen kauyen sa har tonon sa su ke yi.

Akwai wadanda su ke kiran sa da biri, ashe daukaka ta na nan biye da shi, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tashin hankali yayin da mota dauke da fasinjojinta ta fada magudanar ruwa

Mahaifiyar Elie ta ce Ubangiji ya amshi addu’ar ta na ba ta shi da ya yi bayan yaran ta 5 duk sun rasu, kuma ba ta kunyar nuna shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164