Yanzu-Yanzu: Tashin hankali yayin da mota dauke da fasinjojinta ta fada magudanar ruwa

Yanzu-Yanzu: Tashin hankali yayin da mota dauke da fasinjojinta ta fada magudanar ruwa

  • Wata mota ta fada cikin magudanar ruwa a jihar Legas yayin da motar ta kubcewa direban da ke tuka ta
  • An rahoto cewa, wasu fasinjoji sun jikkata kuma ana cire su daga magudanar ruwan, duk da cewa ba a tantance adadinsu ba
  • Har yanzu dai ana ci gaba da kokarin yadda za a ceto fasinjojin da suka fada wannan mummunan ramin

Legas - Wata motar fasinja da ke dauke da fasinjoji ta fada cikin magudanar ruwa da ke unguwar Oworonshoki a jihar Legas.

An bayyana cewa wasu daga cikin fasinjojin sun jikkata a lamarin da ya faru a ranar Litinin 27 ga watan Disamba, Punch ta rahoto.

An yi hadari a jihar Legas
Yanzu-Yanzu: Fasinjoji sun sun fada wani mummunan rami tare da motarsu | Hoto: researchgate.net

An kuma tattaro cewa motar bas din ta kubcewa direban ne kafin ta shiga cikin magudanar ruwa tare da adadin fasinjojin da har yanzu ba a tantance ba.

Kara karanta wannan

Ba zata sabu ba: Iyayen amarya sun fasa aurar da 'yarsu bayan ganin gidan da ango zai aje ta

Ana ci gaba da kokarin ceto fasinjojin da suka makale a ramin zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Cikakken bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel