Da Dumi-Dumi: Burtaniya ta zare Najeriya da wasu kasashe 10 daga masu hatsari

Da Dumi-Dumi: Burtaniya ta zare Najeriya da wasu kasashe 10 daga masu hatsari

  • Bayan taƙaddama, daga karshe Birtaniya ta cire takunkumin hana shiga ƙasarta daga Najeriya da wasu kasashe 10
  • Wannan dai ya faru ne bayan gwamnatin tarayya ta yi barazanar maida nartani na hana kasashen shigowa Najeriya
  • Sabon nau'in cutar korona wato Omicron ya zama barazana ga ƙasashen duniya, inda suke ta faɗi tashin dakile yaɗuwarsa

United Kingdom - Daga ƙarshe gwamnatin ƙasar Birtaniya (UK) ta sake nazari kan hana mutane shiga ƙasarta daga Najeriya da wasu ƙasashe 10.

Dailytrust ta ruwaito cewa hukumomi a Birtaniya sun ƙaƙaba wa waɗan nan ƙasashe 11 dokar hana shiga ne domin dakile yaɗuwar sabon nau'in cutar korona na Omicron.

Sakataren lafiya na Birtaniya, Sajid Javid, shine ya sanar da haka yayin da yake bayani a zauren majalisar kasar ranar Talata.

Omicron
Da Dumi-Dumi: Burtaniya ta zare Najeriya da wasu kasashe 10 daga masu hatsari Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ya shaida wa yan majalisar cewa ƙasar Ingila zata cire kasashe 10 daga jerin masu haɗari daga ƙarfe 04:00 GMT na ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Jami'an DSS da yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga a jihar Katsina

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sakataren lafiyan ya kara da cewa hana mutane shiga daga waɗan na ƙasashe 11 baya hana yaɗuwar da sabon nau'in cutar COVID19 ke cigaba da yi.

Punch ta rahoto yace:

"Ina sanar da ku cewa daga yau zamu cigaba da ɗaukar matakin gwaji na wucin gadi a kan matafiyan da suka shigo daga ƙasashe, kuma zamu cire dokar hana shigowa daga ƙasashe 11 gobe da karfe 4:00 na safe."

Wane kasashe ne UK ta cire?

Kasashen da abun ya shafa sun haɗa da; Angola, Botswana, Eswatini, Lesotho, Malawi, Mozambique, Namibia, Najeriya, Afirka ta Kudu, Zambia da Zimbabwe.

Wannan dai na zuwa ne bayan gwamnatin tarayya ta yi barazanar ɗaukar mataki kan duk kasashen da suka hana yan Najeriya shiga.

Gwamnatin Buhari, wacce ke shan suka daga mutane kan taɓarɓarewar tsaro, ta sha yabo bisa jajircewa a kan bakarta ga waɗan ƙasashe.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamnan Kano, Sanata Kwankwaso, ya yi magana kan rashin tsaro karkashin mulkin Buhari

A wani labari na daban kuma Gwamnatin tarayya ta cika alkawarin da ta daukar wa kungiyar ASUU

Gwamnatin tarayya ta fara cika alkawurran da ta ɗaukarwa kungiyar malaman jami'o'i ASUU kafin ta janye yajin aiki a baya.

Ministan kwadugo, Chris Ngige, yace tunin gwamnati ta tura wa jami'o'i kudin gyara da alawus kimanin biliyan N55.2bn.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262