Budurwa mai shekara 22 za ta yi wuff da tsoho mai shekara 76, tace babu gudu ba ja da baya
- David mai shekaru 76 tare da Claudine mai shekaru 22 da suka yi shekaru hudu suna soyayya suna shirin angwancewa nan babu dadewa
- David ya girma kyakyawar budurwar da shekaru hamsin da hudu cif kuma a wasu lokuta ana masa kallon kakan ta inda ake mata kallon jika
- Duk da abokanansu da jama'a suna caccakar wannan alakar, mahaifan Claudine sun goyi bayan alakar
- Claudine ta sanar da cewa mutane da yawa suna cewa za ta aura David ne saboda ta na son gadon dukiyarsa idan ya mutu, amma ta ce talaka ne
An ce shekaru ba komai bane a soyayya kuma hakan ta ke ga wasu. Labarin soyayyar budurwa Claudine mai shekaru 22 da David mai shekaru 76 babban misali ne na hakan.
David tsoho mai shekaru 76 ya girma matashiyar budurwar da shekaru hamsin da hudu kuma akwai lokuta da dama da ake masa kallon kakanta yayin da ake mata kallon jiksarsa.
Soyayya kadai suka saka gaba
A yayin jawabi ga Afrimax, masoyan biyu sun ce sun fara haduwa ne a coci kuma a take suka fara son juna sannan sun kwashe shekaru hudu tare suna soyayya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
David mai ceto ne a coci kuma ya na yawan addu'a ga Ubangiji da ya albarkacesa da masoyiya kuma wata rana Claudine ta bayyana gare shi.
A take wata murya ta sanar da shi cewa ita ce matarsa. Bai taba aure ba kuma sau da yawa yana kashe lokacinsa ne a cocin.
"Na yi addu'a kuma na yi azumi," yace.
A yayin bayar da labarin ta, matashiyar budurwar tace bayan ta hadu da shi, ba ta taba tsammanin za su fara soyayya ba saboda ganin shi ta ke yi kamar mahaifi.
Claudine ta ce ana ta caccakarsu kan banbancin shekarunsu amma hakan bai taba sauya musu ra'ayinsu ba.
"Dole ne mutane su dinga magana, amma babu abinda zai canza tunda ina kaunarsa. Za su ce ba mu dace ba amma na kan sanar da su cewa soyayya ta isar mana," tace.
Kawayen ta suna ta bata shawarar ta rabu da shi saboda zai mutu ya bar ta sakamakon yawan shekarunsa.
"Ban taba son shi saboda ya mutu ya bar min gado ba," tace.
Sau 7 ina yin warwas a UTME, mahaifina ya rasu, Budurwa ta bada labarinta mai taba zuciya da kayan NYSC
A wani labari na daban, wata budurwa 'yar Najeriya ta gigita yanar gizo da labarin rayuwarta mai matukar taba zuciya bayan ta wallafa murnar ta ta tafiya hidimar kasa.
A yayin wallafa hotunanta inda ta ke sanye da khakin NYSC, @Teeecookie ta rubuta cewa ta kammala karatun sakandare a shekarar 2009 amma ta dinga bajewa a jarabawar UTME.
Sabuwar mai digirin ta ce ta yi jarabawar UTME sau bakwai kafin daga bisani ta samu makin da ake bukata domin samun gurbin karatu a jami'a a shekarar 2016.
Asali: Legit.ng