Beluga, Onavo da wasu kamfanoni 3 da Zuckerberg, mai kamfanin Facebook ya saye
Bayan shekaru 17, hamshakin attajirin dan kasuwan nan na kasar Amurka, Mark Zuckerberg ya canza sunan kamfaninsa na sada zumunta na Facebook zuwa Meta.
Canjin, Mark ya bayyana, an yi shi ne don nuna hangen nesa na kamfanin da abin da yake nufi. Sai dai, ba shine karo na farko ko na biyu da zai canza suna ba, kuma abin sha'awa shine, akwai wasu kamfanoni da Meta ya mallaka.
A cikin wannan rahoton, Legit.ng ta yi tsokaci kan kamfanoni 5 da Mark Zuckerberg da kamfaninsa Meta suka mallaka wadanda suke da girman daraja a kasuwa.
Abin lura ne cewa Meta ya mallaki kamfanoni sama da 10 a karkashinsa.
Ga biyar daga ciki:
1. Beluga
Beluga, manhajar aika sako ce, da watakila za ta iya hamayya da manhajar aike da sako ta Meta idan ba da ba saye ta ba.
Meta ne ya sayi Beluga a ranar 2 ga Maris, 2011, akan kudin da ba a bayyana ba. Shekara guda kenan da kafa ta.
A wancan lokacin Beluga ta kasance tana gudanar da shirin tattara kudade na adadin da ba a bayyana ba. Zai ci gaba da kasancewa daya daga cikin nasarorin da Meta ya samu.
2. Onavo
Investopedia ya kiyasta cewa kudin da aka sayi Onavo ya kai tsakanin dala miliyan 100-200.
An kafa kamfanin na nazarin gidajen yanar gizon wayar hannu mallakar Isra'ila a shekakar 2010 kuma kamfanin Mark na Meta ya samu nasarar saye shi a Oktoba 2013.
Daga baya an cire dandalin daga shagunan sauke manhajojin iOS da Android bayan fuskantar kakkausar suka kamar yadda mutane da yawa suka sanya shi a matsayin manhajar leken asiri.
3. Oculus VR
An saye shi a ranar 25 ga Maris, 2014, Oculus VR kaya ne na fasahar hange da butun-butumi da aka fi sani da 'Virtual Reality' da kamfanin Meta ya saye bayan saye manhajar sakonni ta WhatsApp.
An kiyasta kudin sayansa akan dala biliyan 2.0. Tun lokacin siyansa, Oculus VR ya taka rawa cikin sauri a cikin kasuwar 'Virtual Reality'.
4. WhatsApp
Manhajar WhatsApp na daga cikin garabasar da Meta ta yi nasarar sayewa. Mark ya sayi WhatsApp ne a ranar 19 ga Fabrairu, 2014, kan makudan kudin da suka kai dala biliyan 19.0.
Dandalin na aike da sakon wayar hannu wanda aka kafa a shekarar 2009 zabi ne mai rahusa ga manhajojin aike da sakon rubutu.
An yi imanin cewa da WhatsApp ya kasance babban abokin hamayyar Meta idan da bai saye shi ba.
5. Instagram
Manhajar yada hoto da bidiyo, Instagram wani babban garabasa ne da Meta ta samu. Meta ta sayi Instagram akan kudi dala biliyan 1.0 a ranar 9 ga Afrilu, 2012.
Domin ginawa da habaka dandamali da kansa, Instagram gudana ne shi kadai daban da Meta.
Wasu masana sun kiyasta cewa Instagram yana samar da karin kudaden shiga.
Facebook ya canza suna zuwa Meta, Mark Zuckerberg
A wani labarin, shahrarren shafin ra'ayi da sada zumunta, Facebook, ya sauya suna zuwa Meta daga ranar Alhamis, 28 ga watam Oktoba, 2021.
Kamfanin ya sanar da hakan a shafinsa misalin karfe 7:45 agogon Najeriya da Nijar.
A jawabin da ya kamfanin yayi, ba za'a canza suna manhajar Facebook, Instagram, Messenger da WhatsApp.
Asali: Legit.ng