Insha Allahu bana yan Najeriya zasu yi aikin Hajji, Hukumar jin dadin Alhazai NAHCON
- Kwamishana a hukumar NAHCON ya bayyana cewa da yardar Allah za'a tafi Hajji bana
- Gwamnatin kasar Saudiyya ta sassauta dokokin kariya daga COVID-19 a Makkah da Madina
- Kowace shekara kimanin yan Najeriya 90,000 ke zuwa aikin Hajji
Hukumar jin dadin alhazan Najeriya NAHCON ta bayyana cewa da yardar Ubangiji bana maniyyata a Najeriya zasu samu zuwa kasa mai tsarki don gudanar da aikin Hajji
Wannan ya biyo bayan soke dokokin kariya daga cutar COVID-19 da gwamnatin kasar Saudiyya tayi a farkon makon nan.
Kwamishanan hukumar mai wakiltar al'ummar yankin kudu maso kudu, Musa Sadiq Oniyesaneyene, a hirarsa da Legit Hausa ya bayyana cewa ko makonnin baya ya shiga Saudiyya kuma da yardar Allah bana za'a tafi.
A cewarsa:
"Dubi ga yadda abubuwa ke gudana yanzu, Insha Allahu ya kamata ayi kuma za'a yi.
'"Saboda sassauta dokokin kariya daga cutar Korona a Saudiya da kuma maganar cewa an cire dokar kayyade maniyyata masu shiga Harami, tabbas za'a yi Hajji."
"Ko watanni biyu da suka gabata na tafi Saudiyya wasu ayyuka, mun fuskanci matsaloli, ni kaina na fuskanci wadannan matsaloli amma sai da aka tilasta ni zama a Madina cikin dakin Otal da, hakazalika a Makkah."
"Amma muna kyautata zaton cewa yanzu an cire wadannan dokoki."
An daina bada tazara a sahun Sallah daga Lahadi a Makkah da Madina
Mun kawo muku cewa Hukumomi a Masallatai biyu mafi daraja a duniya sun yi watsi da dokar wajabta baiwa juna tazara yayin Sallah a Masallacin Haram dake Makkah da Masjid Al Nabawi dake Madina.
An yi watsi da wannan doka ne fari daga ranar Lahadi, 17 ga watan Oktoba, 2021.
Sheikh AbdulRahman Sudais ne shugaban Masallatan Biyu.
Wata majiya a fadar Sudais ta bayyana cewa za'a cire dokar bada tazaran ne daga ranar Asabar bayan Sallar Isha, rahoton Haramain Sharifain.
Asali: Legit.ng
Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng
Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng