Da dumi-dumi: Za'a daina bada tazara a sahun Sallah daga gobe Lahadi a Makkah da Madina
- Bayan shekara daya da rabi, za'a koma Sallah kamar yadda aka saba a Makkah
- Bayan kammala Sallar Isha jami'ai suka fara yakice takardun baiwa juna tazara
- Tun bayan bullar annobar Korona, an kayyade adadin masu shiga harami
Saudiyya - Hukumomi a Masallatai biyu mafi daraja a duniya zasu yi watsi da dokar wajabta baiwa juna tazara yayin Sallah a Masallacin Haram dake Makkah da Masjid Al Nabawi dake Madina.
Za'ayi yi watsi da wannan doka ne fari daga ranar Lahadi, 17 ga watan Oktoba, 2021.
Sheikh AbdulRahman Sudais ne shugaban Masallatan Biyu.
Wata majiya a fadar Sudais ta bayyana cewa za'a cire dokar bada tazaran ne daga ranar Asabar bayan Sallar Isha, rahoton Haramain Sharifain.
Hakazalika a daren nan za'a fara cire sitikun da aka manna a kasa don bayyana sahu.
Majiyar ta kara da cewa wurin da aka kebance a baya don masu yi Tawafi da Masaa yanzzu za'a budesu gaba daya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Bugu da kara, za'a mayar da taburmin zama da aka cire kimanin shekaru biyu yanzu.
Za'a daina kayyade adadin masu shiga Masallatan Makkah da Madina
Gwamnatin kasar Saudiyya ta sanar da cewa nan da kwana biyu za'a cire dokokin kayyade adadin wadanda ke shiga cikin Masallatan Makkah da Madina don Ibadah.
Wannan na zuwa kimanin shekaru biyu da aka kayyade adadin masu shiga sakamakon bullar cutar Korona.
Ma'aikatar harkokin cikin gidan Saudiyya ta sanar da cewa fari daga ranar Lahadi mai zuwa, za'a bude Masallatan biyu wa kowa ya shiga.
A cewar Haramain Sharifain, Ma'aikatar tayi sanarwan ranar Juma'a, 15 ga Oktoba, 2021.
Asali: Legit.ng