Aisha Ahmad
1218 articles published since 27 Mar 2024
1218 articles published since 27 Mar 2024
Bidiyon wani yaro wanda har yanzu ba a bayyana shekarunsa ba ya dauki hankali matuka saboda matukar tsayi da ya ke da shi mai ban mamaki. Ana ganin dan Sudan ne.
An tsaiko a shari'ar tsohon Ministan wuta a gwamnatin Muhammadu Buhari, Saleh Mamman saboda rashin lafiya inda ya yanke jiki ya fadi. Alkali ya tausaya masa.
Gwamnatin jihar Zamfara ta amince da fitar biliyoyin Naira domin gina tashar motar zamani a Gusau, inda ake sa ran kashe akalla N4,854,135,954.53.
Tsohon Akanta janar na kasa, Anamekwe Nwabuoku ya roki kotu ta kara masa lokaci domin samun damar mayar da kudin da ake zargin ya wawashe a shekarun baya.
Yayin da ake murna kan janye harajin kan wasu nau'in abinci, gwamnatin tarayya ta ce akwai sharadi kan farashin abinci., inda y ce gwamnati za ta kayyade farashin.
Kungiyar 'yan kasuwa ta kasa (NHTUN) sun bayyana ra'ayinsu kan janye harajin wasu nau'in kayan abinci da za a shigo da su kasar nan da gwamnati ta yi.
Yayin da kungiyoyin ƙwadago su ka dage cewa lallai sai gwamnatin tarayya ta yi ƙari mai gwaɓi kan albashin ma'aikata, shugaban zai gana da kungiyoyi.
Yayin da 'yan Najeriya ke kukan yunwa, ministan noma da samar da abinci, Abubakar kyari ya bayyana ranar karyewar farashin abinci, inda ya ce saura kwanaki 180.
Ana sa ran shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje da matarsa Hafsat da wasu mutum shida za su gurfana a gaban kotu a jihar Kano ranar Alhamis.
Aisha Ahmad
Samu kari