Magu yana sayarwa abokansa wasu kadarorin gwamnati da ya ke ƙwato wa - Fayose

Magu yana sayarwa abokansa wasu kadarorin gwamnati da ya ke ƙwato wa - Fayose

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya yi ikirarin cewa dakataccen mukadashin shugaban hukumar yaki da rashawa ta EFCC, Ibrahim Magu ya rika sayarwa abokansa kadarorin da ya ke kwato wa.

A cewar tsohon gwamnan na jami'yyar PDP, cikin wadanda Magu ke sayarwa kadarorin na gwamnati har da wasu lauyoyi masu rajin kare hakkin bil adama.

Fayose ya bukaci a gudanar da bincike a kan yadda aka sayar da kadarorin da hukumar yaki da rashawar ta yi a karkashin jagorancin Magu.

A cikin sanarwar da ya fitar ta shafinsa na Twitter, tsohon gwamnan kwamitin shugaban kasa da ke binciakar Magu ta fadada binciken ta zuwa mutanen da Magu ya yi aiki tare da su.

Magu ya sayarwa abokansa wasu kayayyakin da ya kwato - Fayose
Ayodele Fayose. Hoto daga The Punch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Ba zan taɓa yin arziki ba muddin ina tare da shi - Matar aure ta garzaya kotu

Ya rubuta, "Ya zama dole a gudanar da cikaken bincike a kan yadda aka sayar da kadarorin da hukumar EFCC ta kwato daga hannun mutane a karkashin jagorancin Magu. An sake ‘sace’ kayan ‘satan’ ne kuma dole da dawo da su.

"Bai kamata a ce ana gudanar da wannan binciken bane kawai domin tsige Magu daga kujerarsa.

"Ya zama dole yan Najeriya su san wadanda suka saya kadarorin da aka kwato da yadda aka sayar da su domin mafi yawancinsu na hannayen daman Magu ne suka siya har da wasu lauyoyi masu rajin kare hakin bil adama.

"Wadannan lauyoyin masu kare hakkin bil adama sune ke goyon bayansa kuma a yau su ne wadanda ke kare shi don sun san idan aka zurfafa bincike a kan abinda Magu ya aikata za a gano abinda suke boye wa daga yan Najeriya.

"Bai kamata a kammala wannan binciken kamar yadda aka saba yi tsakanin wadanda suka san juna.

"Bai kamata a dakata saboda an cire shi daga ofishinsa ba, tsige Magu bai gamsar da mu ba. Ya zama dole a kwato kadarorin da aka sace kuma a hukunta wadanda suka saya kayan satar.

"Ya kamata a tona asirin dukkan wadanda ke ajiye wa Magu kudade da wadanda ke taimaka masa wurin almundahanar kudi."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel