Babban Hafsan tsaron Najeriya ya tabbatar da kisan Shugaban ISWAP, Mus'ab Albarnawy
- Bayan wata guda da yaduwar labarin, hukumar Soji ta tabbatar da kisan Albarnawy
- Albarnawy ya kasance Shugaban yan ta'addan ISWAP
- Shine dan wanda ya assasa Boko Haram, Muhammad Yusuf
Abuja - Babban Hafsan tsaron Najeriya (CDS), Janar Lucky Irabor, ya tabbatar da kisan shugaban kungiyar yan ta'addan daular Islamiyya a yammacin Afrika ISWAP, Abu Musab Al-Barnawi.
Janar Irabor ya bayyana hakan ne ranar Alhamis yayinda hira da manema labarai da fadar shugaban kasa ta shirya a AsoVilla, Abuja, DailyTrust ta ruwaito.
Irabor yace:
"Ina mai tabbatar muku cewa Abu Mus'ab ya mutu. Ya mutu kuma ba zai taba tashi ba."
An hallaka Shugaban yan ta'addan ISWAP, AlBarnawy
Bayan shekaru da dama ana farautarsa, an samu nasarar hallaka shugaban yan ta'addan ISWAP Mus'ab Albarnawy a jihar Borno, rahoton DailyTrust.
An samu rahoton cewa an kashe Albarnawy ne a karshen watan Agustan 2021.
Mus'ab Al-Barnawi ne 'dan mu'asassin Boko Haram, Mohammed Yusuf, wanda shine jami'an tsaro suka kashe a 2009 yayinda yayi fito-na-fito da gwamnati.
A shekarar 2016, kungiyar ISIS ta alanta Albarnawy a matsayin shugabanta na yankin Afrika ta yamma.
Ta yaya aka kashe Al-Barnawi?
An samu riwayoyi biyu game da labarin mutuwarsa. Yayinda riwayar farko tace Sojojin Najeriya ne suka hallakashi, wata riwayar tace rikicin cikin gida tsakaninsa da sauran yan ta'addan ISWAP yayi sanadiyar mutuwarsa.
Riwayar farko ta dogara ne kan maganganun wasu jami'an tsaron dake faggen fama inda sukayi ikirarin cewa an hallakashi ne tare da wasu kwamandojin ISWAP kimanin biyar.
Wata majiya ta bayyana cewa an kasheshi a Bula Yobe, wani gari dake iyakan jihar Yobe da Borno.
Amma wata majiyar daban ta ce ya mutu ne a Yale, Bama.
Asali: Legit.ng