Jam'iyyar PDP ta maida zazzafan martani kan ikirarin da APC ta yi game da zaɓen Najeriya

Jam'iyyar PDP ta maida zazzafan martani kan ikirarin da APC ta yi game da zaɓen Najeriya

  • Babbar jam'iyyar hamayya PDP ta maida zazzafan martani kan maganar da APC ta yi game da ɓangaren zaɓe a ƙasar nan
  • Kakakin PDP, Kola Ologbondiyan, yace kamata ya yi APC ta rungumi gazawarta hannu biyu ba wai ta rinka kokawa ba
  • Ya kuma yi kira ga yan Najeriya da su cigaba da baiwa jam'iyyar PDP goyon baya a kokarin da take na ceto ƙasar nan daga hannun APC

Abuja - Babbar jam'iyyar adawa PDP ta kirayi APC mai mulki ta amince da gazawarta a gwamnatance kuma ta daina damun yan Najeriya da koke-koke kan wasu matsaloli.

PDP ta faɗi haka ne yayin da take martani kan ikirarin jam'iyyar APC mai mulki cewa ta haɓɓaka tare da gyara ɓangaren gudanar da zaɓe a ƙasa, kamar yadda dailytrust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Babban dalilin da yasa yan Najeriya ba zasu amince da Igbo ya zama shugaban ƙasa a 2023 ba, Dokpesi

Kakakin jam'iyyar PDP na ƙasa, Kola Ologbondiyan, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.

Jam'iyyar APC da PDP
Jam'iyyar PDP ta maida zazzafan martani kan ikirarin da APC ta yi game da zaɓen Najeriya Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

APC ce ta lalata komai a Najeriya

Ologbondiyan yace:

"Abinda ya mamaye ƙasar mu ba shi da daɗin sauraro, APC ta ruguza mana tattalin arziki, ɓangaren zaɓe da kuma haɗin kan ƙasa, har takai ga rayuwa ta yi kunci ga yan Najeriya."

Yace kamata ya yi tun yanzun APC ta fara shirin miƙa lamarin jagoranci saboda yan Najeriya sun gaji hakanan, kuma basu shirya cigaba da zama a haka har bayan 2023 ba.

Zamu ceci Najeriya daga APC

Kakakin jam'iyyar PDP ya yi kira ga yan Najeriya da su cigaba da nuna goyon bayansu m ga jam'iyyar PDP yayin da ta kammala shirin ceto Najeriya.

A cewarsa tuni PDP ta shirya kwato Najeriya daga hannun mulkin APC na rarraba kan al'umma da rashin kwarewa.

Kara karanta wannan

Yar majalisar dattijai ta fice daga PDP ta koma jam'iyyar APC, Ta bayyana dalilai

A wani labarin kuma Manyan makusantan Gwamna sun sauya sheka zuwa jam'iyyar hamayya PDP

Mutum biyar daga cikin mataimakan gwamnan Anambra, Willie Obiano , sun fice daga jam'iyyar APGA, sun koma PDP.

Bayan ficewarsu daga APGA zuwa PDP , waɗanda suka sauya shekan sun sha alwashin tallafawa ɗan takarar gwamna, Valentine Ozigbo, domin ya samu nasara a zaɓen dake tafe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel