Shugabancin PDP: Taron shugabannin jam’iyyar na arewa ya hadu da gagarumin cikas

Shugabancin PDP: Taron shugabannin jam’iyyar na arewa ya hadu da gagarumin cikas

  • Taron shugabannin jam’iyyar Peoples Democratic Party na arewa da aka shirya gudanarwa a ranar Laraba, 13 ga watan Oktoba, ya hadu da cikas
  • Mambobin kungiyar da ake sanya ran za su halarci taron a Abuja duk sun ki zuwa saboda wasu dalilai da ba a bayyana ba
  • Shugaban kwamitin, Umaru Fintiri, ya sanar da dage taron don shugabannin su ci gaba da tuntuba

Abuja Yayinda shirye-shirye ke kara kankama gabannin zaben 2023, shugabannin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na arewa sun gudanar da wani taro a shirin tunkarar babban taron jam’iyyar.

An shirya gudanar da taron ne a masaukin gwamnan jihar Bauchi da ke Abuja a ranar Laraba, 13 ga watan Oktoba, inda shugabannin za su cimma matsaya kan babban taron jam’iyyar da ke zuwa.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda jami’an yan sanda suka tsere yayin da yan bindiga suka mamaye fadar sarkin Ogun yayin taron APC

Shugabancin PDP: Taron shugabannin jam’iyyar na arewa ya hadu da gagarumin cikas
Shugabancin PDP: Taron shugabannin jam’iyyar na arewa ya hadu da gagarumin cikas Hoto: Governor Fintiri
Asali: Facebook

Shugabannin jam’iyyar sun ki hallara a wajen taron

Sai dai kuma, Channels ta rahoto cewa mambobin PDP da ake sanya ran za su halarci taron sun kaurace wa lamarin.

Da yake jawabi ga wasu shugabannin da suka hallara a wajen taron, shugaban kwamitin shirya taron, Umaru Fintiri ya dage taron.

Fintiri wanda ya kasance gwamnan jihar Adamawa ya ce an dage taron ne domin ba wasu mambobi dama don ci gaba da tuntuba.

Manufar taron da aka sake dagewa

Jaridar The Nation ta kuma rahoto cewa shugabannin jam’iyyar daga arewa sun gana don tabbatar da ganin cewa an rage yawan mukaman shugabanci na PDP da aka mika yankin arewa.

Don cimma wannan, shugabannin jam’iyyar na arewa sun yanke shawarar kafa kwamitin mutum 20 da nufin rage yawan ‘yan takara daga kowanne daga cikin yankunan.

Kara karanta wannan

2023: Saraki ya shirya fafatawa da Atiku yayin da Kawu Baraje yace PDP za ta mika tikiti zuwa Arewa

Bugu da kari, shugabannin PDP a yankin arewa ta tsakiya suma sun gana sannan sun cimma matysaya wanda ya kai ga bayyanar Iyorchia Ayu a matsayin dan takarar kujerar shugabancin jam’iyyar.

An yi ittifaki kan Shema, Suleiman Nazif, da Ayu matsayin mutum 3 da zasuyi takarar kujeran shugaban PDP

A gefe guda, mun ji cewa adadin masu takarar neman kujeran Shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP ya sauko daga goma zuwa uku bayan an bukaci kowani yanki cikin yankunan Arewa uku su gabatar da mutum daya.

Tsohon Shugaban majalisar dattawa, Iyiochia Ayu, a ranar Talata ya zama dan takarar da zai wakilci yankin Arewa maso tsakiya bayan Sanata David Mark ya hakura.

Hakazalika tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shema, ya zama wanda zai wakilci Arewa maso yamma bayan lashe kwarya-kwaryar zaben da akayi tsakaninsa da tsohon gwamnan Kaduna, Ahmed Makarfi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel