El-Rufai ya nada babban abokin dan sa matsayin mai gudanarwar 'ƙasar' Kaduna
- Gwamna Nasir El-Rufai ya kirkiri hukumomin gudanarwa 3, ya nada babban abokin dan shi, Bello El-Rufai a matsayin shugaban na birnin Kaduna
- Tun farkon mulkin El-Rufai, ya nada Hafiz Bayero a matsayin mai ba shi shawara ta musamman kan al'amuran gwamnati, daga bisani ya koma harkokin kasuwa
- A ranar Litinin, Muyiwa Adekeye ya sanar da kirkirar hukumomin gudanarwa na Zaria, Kaduna da Kafanchan kuma majalisa ta aminta da su
Kaduna - Muhammad Hafiz Bayero, babban abokin Bello El-Rufai, babban dan gwamnan jihar Kaduna, shi ne Gwamna Nasir El-Rufai ya nada a matsayin mai gudanarwar kasar Kaduna da ya kirkira.
Kasar ta na daya daga cikin ukun da gwamnatin Malam Nasir ta kirkira a cikin makon nan a jihar, Daily Trust ta wallafa.
A yayin sanar da nadin Bayero, Muyiwa Adekeye, mai magana da yawun gwamnan, ya ce majalisar jihar ta amince da dokar kafa hukumomin kula da kasar Kaduna, Kafanchan da Zaria a matsayin birane.
Daily Trust ta ruwaito cewa, ya sanar da nadin sauran masu gudanarwan biyu masu matsayi daya da Bayero a ranar Litinin.
Su ne Balaraba Aliyu-Inuwa, mai gudanarwa ta kasar Zaria da kuma Phoebe Sukai Yayi, mai gudanarwa ta kasar Kafanchan.
Sukai babbar ma'aikaciyar gwamnati ce wacce ta kai har matsayin sakatariyar ma'aikatar ilimi a jihar Kaduna.
A baya, Bayero ya yi aiki a matsayin mai bada shawara na musamman ga Gwamna El-Rufai kan al'amuran gwamnati na dukkan matakai.
A matsayin mai bada shawaran, shi ne ke da alhakin kula da alaka tsakanin gwamnati da masu saka hannayen jari da kuma abokan cigaba.
Daga bisani, ya koma manajan daraktan cibiyar habaka kasuwanni na jihar Kaduna.
Ya shiga gwamnatin Malam El-Rufai a watan Yunin 2015 a matsayin babban mataimaki a fannin kirkirar ayyuka. Ya na daga cikin tawagar da aka fara kafa cibiyar kwadaitar da saka hannayen jari na Kaduna.
El-Rufai ya nada Khalil mai shekaru 28 matsayin shugaban KADIPA
A wani labari na daban, Malam Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna ya nada Khalil Nur Khalil mai shekaru 28 a matsayin shugaban cibiyar habaka zuba jari ta jihar Kaduna, KADIPA.
Khalil ya kammala digirinsa daga jami'ar Eastern Mediterranean da ke kasar Cyprus inda ya karanci kasuwanci da tattalin arziki.
TheCable ta ruwaito cewa, kafin wannan nadin, Khalil ne daraktan zuba jari a KADIPA, matashi mafi karancin shekaru da ya taba samun wannan matsayin a tarihin jihar Kaduna.
Asali: Legit.ng