Shekara ta 15 kacal, ku bani masauki, ƙaton saurayi ɗan Najeriya ya roƙi jami’an filin jirgi a Ingila
- An kwashi ‘yan kallo bayan wani katon saurayi ya fadi guiwa kasa ya na rokon jami’an tsaro a filin jirgin sama dake Ingila
- Kamar yadda bidiyon ya nuna, saurayin ya ce shekarun sa 15 kacal kuma ya bukaci su taimaka ma sa kada ya dawo Najeriya
- Hakan ya biyo bayan sun gano takardun sa na bogi ne, daga nan ya bukaci su adana shi don maraya ne shi mai karancin shekaru
Ingila - Mutane sun taru su na ba idanun su abinci bayan wani lamari mai ban dariya ya auku a filin jirgin sama na Heathrow da ke Ingila yayinda wani katon saurayi wanda ya zo daga Najeriya ya bayyana wasu takardun bogi.
Mutumin, Okpegwa Benson, bayan shan tambayoyi ya duka kasa cike da hawaye inda ya ce musu shekarun sa 15 kuma wani mutumin kirki ne ya ba shi takardun fasfo din.
Na yi gyaran kwata ana biya na N20: Ɗan kwallo mafi tsada a Afirka kuma tauraron Super Eagles, Victor Osimhen
Bayan shan tambayoyi ne ya ci gaba da bayyana cewa ‘yan fashi ne su ka halaka iyayen sa don haka rayuwar sa ta na cikin hatsari matsawar ya koma Najeriya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Da farko cewa ya yi yana aiki a Ingila
Bidiyon wanda Real Responders su ka wallafa a shafin su na Facebook, ya nuna da farko yadda Okpegwa Benson ya sanar da wata ma’aikaciya a filin jirgi mai suna Bahli Rupri cewa ya na da takardun sa kuma har aiki yake yi a Ingila.
Lamarin ya koma wasan a sha ruwan tsintsaye bayan gano cewa takardun Benson na bogi ne, daga nan ne ya canja labarin.
Bayan nan ne ya ce shekarun sa 15 kuma iyayen sa duk sun rasa ran su don haka ya bukaci jami’ar filin jirgin ta taimaka ma sa.
Bayan Benson ya ga su na tambayar sa a hankali ne ya sa ya yi amfani da damar sa ya ce bai wuci shekaru 15 ba.
A cewar sa ‘yan fashi ne su ka halaka iyayen sa kuma rayuwar sa ta na cikin hatsari matukar aka mayar da shi Najeriya.
Daga nan ne jami’an tsaron su ka mika shi ga jami’an kulawa da baki na Ingila inda aka sama ma sa masauki a kudancin Ingila.
Bayan nan ne aka nemi Benson sama ko kasa ba a gan shi ba.
Abi da mutane suka ce game da lamarin
Mutane da dama sun yi ta tsokaci iri-iri karkashin wannan wallafar inda wani Christain Fuseini Abusigri ya ce:
“Yanzu haka rayuwa ta mayar da ‘yan Afirka, abin kunya ne ace saboda mugayen shugabanni ba ma iya zama cikin kwanciyar hankali a kasashen mu. Su kan su shugabannin mu ai abin kunya ne a gare su tunda ba sa amfanar mu da komai.”
Ebuka Onyekwere kuwa ya ce:
“Gaskiya tsarin mulkin su ya yi, kalli yadda su ka ba shi matsuguni duk da sun san karya yake yi."
Hotunan bikin: An shafa Fatihar Saurayi da budurwan da suka hadu a Twitter
A wani labarin, kun ji wasu masoya, Ameenu da Yetunde, sun bayyana wa mutane yadda su ka hadu har soyayyar su ta kai su ga aure a kafar sada zumuntar zamani.
Kamar yadda Ameenu ya wallafa wani hoto bisa ruwayar Legit.ng, inda ya nuna yadda hirar su ta kasance bayan lokacin da ya tura wa Yetunde sako a 2018.
Ameenu ya bayyana yadda ya fara ne da gabatar wa da Yetunde kan sa bayan ya tambayi yadda take.
Asali: Legit.ng