‘Yan sanda sun yi ram da wani sojan bogi, mai yi wa mata sata da sunan zai aure su

‘Yan sanda sun yi ram da wani sojan bogi, mai yi wa mata sata da sunan zai aure su

  • ‘Yan sanda sun kama Mkwatula, mai shekaru 38 wanda ya ke yi wa mata sata bayan dankara mu su karya
  • Yana cewa shi sojan Malawi ne kuma ya je gare su ne da alkawarin zai aure su daga nan ya yashe su
  • Cikin matan akwai wadanda ya sace wa babura, talabijin, barguna, wayoyi har ma da kudade masu tarin yawa

Malawi - ‘Yan sanda sun kama Mkwatula mai shekaru 38 bisa yi wa tarin mata sata bayan dankara mu su karyar shi sojan Malawi ne kuma auren su ze yi bisa ruwayar LIB.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Ntcheu, Rabecca Kwisongole ta ce wanda ake zargin ya dade ya na yaudarar mata da soyayya da kuma alkawarin auren su.

‘Yan sanda sun yi ram da wani sojan bogi, mai yi wa mata sata da sunan zai aure su
Sojan bogi da aka kama yana yaudarar mata yana musu sata. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

An sha mamaki bayan gano cewa gardin namiji aka tura gidan yari na mata ba tare da an gane a kotu ba

A cewar Kwisongole, bayan kwanaki da mika tayin soyayyar sa ga mace, Mkwatula zai lallaba ya sace mu su abubuwa masu daraja kamar babura, talabijin, wayoyi, barguna har kudade ma.

Kwanaki kadan da fara soyayya sai ya lallaba ya yi sata

Kamar yadda LIB ta ruwaito, Kwisongole ta ce:

“Yan sanda sun tattaro bayanai akan yadda mata 3 su ka kai korafi akan sa kuma ana sa ran zai bayyana a gaban kotu don ya amsa tambayoyi dangane da sata da kuma yaudarar da ya yi da ta ci karo da sashi na 278 fa 161 na Penal Code.”

Sai dai ‘yan sanda sun samu nasarar ceto babur, babban talabijin na bango, waya, bargo da sauran su.

Wanda ake zargin dan kauyen Mdala ne dake Amidu a yankin Balaka.

'Yan sanda sun damƙe dodanni biyu kan laifin aikata fashi da makami

Hakazalika, kun ji cewa, Rundunar 'yan sandan Nigeria reshen jihar Ondo ta yi nasarar cafke wasu dodanni biyu kan yi wa mazauna unguwar Melege a karamar hukumar Owo ta jihar fashi.

Kara karanta wannan

Na yi gyaran kwata ana biya na N20: Ɗan kwallo mafi tsada a Afirka kuma tauraron Super Eagles, Victor Osimhen

An kama dodannin biyu da aka ce sunansu Sheriff Ojo da Muhammed Lukman bayan sun yi wa wani Adinoyi Mohammed fashin N370,000 da wayarsa ta salula, rahoton Vanguard.

Ruwayar jaridar Daily Trust ya ce mai magana da yawun 'yan sandan jihar Ondo, Funmi Odulami ta tabbatar da afkuwar lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164