Karshen PDP da APC: Jam'iyyu 7 za su hadu don kwace tasirin APC da PDP a Najeriya

Karshen PDP da APC: Jam'iyyu 7 za su hadu don kwace tasirin APC da PDP a Najeriya

  • PDP da APC za su fuskanci gagarumar adawa daga wasu jam’iyyun siyasa gabanin zaben 2023
  • Mai neman takarar shugaban kasa, Kingsley Moghalu, ya ce akalla jam'iyyu bakwai ne za su hade don kafa adawa mai karfi a lokacin zaben
  • Moghalu a ranar Litinin, 13 ga watan Oktoba, ya ce lokaci ya yi da zaben Najeriya zai daina kasancewa game da jam’iyya mai mulki da na adawa kawai

Kingsley Moghalu, mai neman takarar shugaban kasa a 2023 a karkashin jam'iyyar African Democratic Party (ADC) ya bayyana cewa kimanin jam'iyyu bakwai na shirin kafa babbar jam'iyya gabanin zabe mai zuwa.

Moghalu ya ce babbar jam'iyyar za ta kasance wani dandali ga matasan Najeriya wadanda ke da niyyar shiga harkokin shugabanci maimakon jam'iyyun All Progressives Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP) kawai, jaridar The Nation ta rahoto.

Read also

2023: Matasan APC sun bayyana wanda za su marawa baya a zaben Shugaban kasa

Karshen PDP da APC: Jam'iyyu 7 za su hadu don kwace tasirin APC da PDP a Najeriya
Karshen PDP da APC: Jam'iyyu 7 za su hadu don kwace tasirin APC da PDP a Najeriya HoKingsley Moghalu
Source: UGC

Ya bayyana amincewar da Majalisar Dattawa ta yi na watsa sakamakon zabe ta na’ura a matsayin alamun cewa babban zabe mai zuwa zai kasance sahihi.

Masanin na tattalin arziƙin siyasa ya bayyana cewa hadaddun ra'ayoyi da hanyar isa ga talakawa yana daga cikin abin da ya sa ADC ta zama ta daban.

Ya kara da cewa jam’iyyar za ta hade da jam’iyyu kusan shida ko bakwai don zaben shugaban kasa.

Kalamansa:

“Sabo da haka, na yi imanin cewa zaben 2023, bai kamata ‘yan Najeriya su bari a yi takara tsakanin bangarori biyu da aka saba ba saboda babu wani bambanci. Yakamata ya zama yaƙi tsakanin tsohuwa da sabuwar Najeriya. Wannan shine abin da yakamata 2023 ta kasance."

2023: Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Moghalu ya fice daga jam'iyyar YPP ya koma sabuwar jam'iyya

Read also

Dan majalisa ya hango matsala, ya ce APC na kitsa magudi a zaben 2023

A gefe guda, mun kawo a baya cewa tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Young Progressive Party (YPP), Kingsley Moghalu ya koma jam'iyyar Action Democratic Congress (ADC) gabanin babban zaben 2023.

Kingsley Moghalu ya bayyana hakan ne a shafinsa na dandalin sada zumunta ta Facebook a ranar Juma'a inda ya rubuta cewa, "An kammala komai a hukumance."

Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Nigeria, CBN, ya kuma wallafa wata sabuwar fosta dauke da hotonsa da tambarin sabuwar jam'iyyarsa.

Source: Legit Nigeria

Online view pixel