2023: Matasan APC sun bayyana wanda za su marawa baya a zaben Shugaban kasa

2023: Matasan APC sun bayyana wanda za su marawa baya a zaben Shugaban kasa

  • Abubakar Sadiq Fakai yace za su goyi bayan duk matashin da ya tsaya takara
  • Fakai shi ne shugaban matasan jam’iyyar APC na yankin Arewa maso yamma
  • Matashin yace sa’o’insa suka cika APC, kuma ba ya goyon bayan karba-karba

Kaduna - Matasan jam’iyyar APC na shiyyar Arewa maso yamma sun sha alwashin mara baya ga duk wani matashi da ya nemi takarar shugaban kasa a 2023.

Daily Trust ta rahoto shugaban matasan APC na Arewa maso yamma, Abubakar Sadiq Fakai, yana wannan bayanin a ranar Laraba, 13 ga watan Oktoba, 2021.

Honarabul Abubakar Sadiq Fakai yace mata da matasa sun kai kusan kashi 70% na magoya miliyan 40 da suka yi rajista da APC a fadin jihohin kasar nan.

Kara karanta wannan

Karshen PDP da APC: Jam'iyyu 7 za su hadu don kwace tasirin APC da PDP a Najeriya

Haka zalika jagoran matasan yace matasan ne kimanin 55% na shugabannin da aka nada daga zabukan shugabannin APC na mazabu da kananan hukumomi.

Abubakar Sadiq Fakai yake cewa babu abin da zai hana matasan jam’iyyar APC takwaransu idan har ya fito neman wata kujera, har da ta shugaban kasa a 2023.

Hon. Fakai ya kara da cewa ba su da niyyar fada ko kalubalantar shugabanninsu da ke harin shugaban kasa, yace kuma ba za su yi abin da ya saba doka ba.

'Ya 'yan APC
Gangamin APC a zaben 2019 Hoto: silvernewsng.com
Asali: UGC

Karba-karba ko cancanta a zabe?

A game da tsarin karba-karba da ake kokarin shigo da shi a zabe mai zuwa, Abubakar Fakai ba ya goyon-bayan wannan shiri, yace kamata ya yi a duba cancanta.

“Abin da muka sani shi ne ana yin karba-karba ne idan an samu fahimta tsakanin shugabanni. Kuma jam’iyya ba ta san da zaman karba-karba ba.”

Kara karanta wannan

Manyan ƴan siyasan arewa 5 da suka yi rantsuwar ba za su sauye sheƙa ba amma suka saɓa

“A zaben fitar da gwanin da aka yi a 2014, an zabi ‘dan takara ne lura da cancanta da yiwuwar ya iya lashe zaben da za ayi.” - Abubakar Sadiq Fakai

A madadin matasan yankin, Fakai yace lokaci ya yi da APC a matsayinta na jam’iyya mai son kawo cigaba, za ta zakulo ‘dan takarar da zai iya kawo mata kuri’u.

APC ta bangare a Kano

Kuna da labari cewa Ibrahim Shekarau, Barau Jibrin, Sha'aban Sharada da wasu jiga-jigan kusoshin APC na jihar Kano sun zauna da Gwamna Mai Mala Buni.

Jam’iyyar APC ta barke a Kano yayin da wadannan jagorori suka ja daga da Gwamna Abdullahi Ganduje. Daga baya Kabiru Gaya ya zare kansa daga wannan tafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel