Jerin wayoyi 20 da ke bukatar inganta zubin kwakwalwa saboda matsala da WhatsApp
WhatsApp, shahararriyar manhajar aike da sakonni mallakar Facebook, na sabunta tsarin manhajar saboda haka kamfanin ya sanar da cewa wasu wayoyin iPhone za su bukaci inganta zubin kwakwalwa zuwa babban zubi don ci gaba da tafiya daidai da bukatar WhatsApp.
Kamar yadda The Guardian ta ruwaito, kamfanin ya bayyana cewa zai toshe ayyukansa ga wasu tsoffin na'urori farawa daga 1 ga Nuwamba.
Ya lura cewa masu amfani da wayoyin iPhone wadanda suka saya tun kafin 2016 dole ne su inganta zubin kwakwalwar wayoyinsu zuwa akalla iOS 10.
Haka kuma, Businessinsider ya bayyana cewa manhajar WhatsApp din za ta dace kadai ne da na'urorin da ke aiki akan zubin kwalkwalwa na KaiOS 2.5.1 ko sama, wadanda suka hada da JioPhone da JioPhone 2.
Jerin wayoyi 20 da ke bukatar inganta zubin kwakwalwa
Daga rahotannin da ta tattaro, Legit.ng ta hada jerin wayoyin da za su bukaci wannan ingantawa cikin gaggawa kamar haka:
- iPhone 5
- iPhone 5C
- iPhone 5S
- iPhone 6
- iPhone 6 Plus
- iPhone SE (1st-gen)
- iPhone 6S
- iPhone 6S Plus
- iPhone 7
- iPhone 7 Plus
- iPhone 8
- iPhone 8 Plus
- iPhone X
- iPhone XR
- iPhone XS
- iPhone XS Max
- iPhone 11
- iPhone 11 Pro
- iPhone 11 Pro Max
- iPhone SE (2nd-gen)
Cikin sa’o’i kadan da dakatar da Facebook, Zuckerberg ya tafka asarar $6bn, ya koma na 5 a jerin biloniyoyi
A bangare guda, wanda ya kirkiro kafar sada zumuntar zamani ta Facebook, Mark Zuckerberg ya tafka asarar fiye da $6,000,000,000 cikin sa’o’i kadan da dakatar da kafar, inda ya sauka kasa a jerin masu kudin duniya kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Lamarin da ya janyo asarar ta auku ne cikin sa’o’i kadan kwatsam kafafen sada zumuntar zamani kamar Facebook, Facebook Messenger, Instagram da WhatsApp su ka tsaya cak su ka dena yin aiki.
Kamar yadda Yahoo Finance ta ruwaito, wannan lamarin da ya auku a ranar ranar Litinin 3 ga watan Oktoban 2021.
Asali: Legit.ng