Gwamnatin tarayya ta saki sunayen mutum 10,000 da zata baiwa bashin NYIF

Gwamnatin tarayya ta saki sunayen mutum 10,000 da zata baiwa bashin NYIF

  • Ministan Matasa ya bayyana adadin matasan da za'a baiwa sabon bashin jari
  • Ministan yace za'a basu horo na musamman don tabbatar da sun kashe kudin yadda ya kamata
  • Wannan shine zango na biyu na shirin NYIF da gwamnatin ta kaddamar

Abuja - Gwamnatin tarayya a ranar Talata, ta ce an sake sakin sunayen mutum 10,000 da za'a baiwa tallafin kudin jari karkashin shirin Tallafin matasa a Najeriya (NYIF).

Gwamnatin tace wannan ya biyo bayan mutum 5,285 da aka saki sunayensu da farko.

Wannan na kunshe cikin jawabin da Kola Daniel, mai magana yawun Ministan wasanni da matasa, Sundaye Dare, ya saki, rahoton Tribune.

Ya bayyana cewa za'a horar da wadanda aka zaba kuma za'a raba musu kudaden da akayi alkawari.

Jawabin Ministan ya kara da cewa an zabi sunayen matasan ne bayan tantance matasa milyan uku da suka nemi bashin.

Kara karanta wannan

Tunde Bakare ya yi magana game da shirin takarar 2023 bayan ya sa labule da Buhari

Yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Bayan kammala sahun fari, NIRSAL ya fitar da sunayen mutane 10,000 don horar da su da kuma basu kudin jarin."
"Bashin da za'a bada ya fara daga dubu dari biyu da hamsin 250,000 zuwa milyan uku (N3,000,000)
"Wadannan sunaye na kan shafin FMYSD da NOYA."
"Dukkan wadanda aka zaba zasu yi horo don tabbatar da cewa sun yi amfani da bashin yadda ya kamata."

Gwamnatin tarayya ta saki sunayen mutum 10,000 da zata baiwa bashin NYIF
Gwamnatin tarayya ta saki sunayen mutum 10,000 da zata baiwa bashin NYIF Hoto: Ministry of Sports
Asali: UGC

Mun rabawa matasan Najeriya 7,057 tallafin N3bn ta shirin NYIF, CBN

Babban bankin Najeriya (CBN), yace a shirin da yake yi tare da ma'aikatar matasa da wasanni, kawo yanzu an rabawa matasan Najeriya 7,057 kudi N3bn.

An yiwa shirin take 'Asusun lamunin matasan Najeriya' (NYIF).

Wannan na kunshe cikin rahoton da CBN ya wallafa a shafinsa ranar Litinin, 11 ga Okotba, 2021.

Kara karanta wannan

A tura matasan NYSC faggen yaki da yan bindiga, wanda ba zai je ba a daina biyansa albashi

A cewar rahoton, wadanda suka amfana da wannan kudi sun hada da daidaikun mutane 4,411, da kuma masu kananan sana'o'i 2,646.

Asali: Legit.ng

Online view pixel