Abun da ciwo sosai, Tsohon kwamishina ya fice daga jam'iyyar hamayya PDP

Abun da ciwo sosai, Tsohon kwamishina ya fice daga jam'iyyar hamayya PDP

  • Tsohon kwamishina kuma babban jigo a jam'iyyar PDP reshen jihar Kuros Ribas, Edem Ekong, ya miƙa takaradar murabus daga mamban jam'iyya
  • Ekong, ya bayyana cewa ya ɗauki dogon lokaci yana nazari kan matakin da ya kamata ya ɗauka, daga karshe yagano bashi da wani zaɓi sai wannan
  • A cewar tsohon kwamishinan wannan matakin yana da ciwo kuma yana da tsantsar dana sani, amma ba shi da wani zabi

Cross Rivers - Jigon babbar jam'iyyar hamayya PDP reshen jihar Kuros Ribas, Edem Ekong, ya fice daga jam'iyyar, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Ekong, ya sanar da ficewarsa daga PDP ne a wata takardar murabus daga mamban jam'iyya da ya aike wa shugaban gundunamarsa, Idundu/Anyanga-Nse, ƙaramar hukumar Akpabuyo.

Jam'iyyar hamayya PDP
Abun da ciwo sosai, Tsohon kwamishina ya fice daga jam'iyyar hamayya PDP Hoto: thenewsguru.com
Asali: UGC

A cikin wasikar, wanda akai wa take da, 'Murabus daga mamban jam'iyyar PDP,' Mista Ekong yace:

Kara karanta wannan

Babban dalilin da yasa yan Najeriya ba zasu amince da Igbo ya zama shugaban ƙasa a 2023 ba, Dokpesi

"Cike da takaici da tsantsar dana sani ina mai sanar da murabus ɗina daga mamba a jam'iyyar PDP."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Murabus daga PDP a gundumar Idundu/Anyanga-Nse dake ƙaramar hukumar Akpabuyo, a cikin jihar Kuros Ribas."
"Na ɗauki wannan matakin ne bayan dogon nazari kan abubuwa da dama, daga ƙarshe ya zamana bani da wani zabi sai na yin murabus."

Ekong ya rike mukamai da dama

Mista Ekong ya taba rike muƙamin kwamishina na zango ɗaya, inda ya jagoranci ma'aikatar ƙasa.

Hakanan tsohon mamban jam'iyyar PDP ya taba rike mukamin darakta janar na sashin kula da jama'a da tafiye-tafiye, duk a jihar ta Kuros Ribas.

A wani labarin na daban kuma Manyan jiga-jigan APC mai mulki da dubbannin mambobi sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP

Dailytrust ta rahoto sanata mai wakiltar Benuwai ta kudu, Abba Moro, na cewa jam'iyyarsa ta PDP ce kaɗai zata iya magance matsalolin Najeriya.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Mambobin Jam'iyyun Hamayya Sama da 5,000 Sun Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar APC

Sanatan, wanda ya yi jawabi wajen bikin tarbar masu sauya sheƙan, yace Najeriya ta rasa komai ƙarƙashin jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262