Bidiyon saurayin da ya bata rai bayan budurwar da ya gayyata cin ‘Pizza’ ta zo da wasu kawayenta biyu

Bidiyon saurayin da ya bata rai bayan budurwar da ya gayyata cin ‘Pizza’ ta zo da wasu kawayenta biyu

  • Wani mutum ya kasance cikin takaici bayan wata budurwa da ya gayyata don shakatawa ta bayyana tare da wasu kawayenta guda biyu
  • A cikin bidiyon da ya shahara, alamu sun nuna cewa mutumin bai ji dadi ba saboda bai taɓa abincin da ke gabansa ba kuma ya bata fuska
  • Mutane da yawa da suka kalli bidiyon sun caccaki budurwar kan yadda ta zo tare da kawaye, wasu sun fadi abin da za su yi idan suka tsinci kansu a wannan halin

Yanayin wani saurayi bayan budurwar da ya gayyata cin abinci ta iso tare da wasu kawayenta biyu ya haddasa cece-kuce a shafin soshiyal midiya.

Wani ɗan gajeren faifan bidiyo wanda Wisdom Blogg ya yada akan shafin Instagram ya nuna mutumin yayin da ya yi kicin-kicin da fuska inda yan matan ke jin daɗin pizarsu ba tare da kula da yanayinsa ba.

Read also

Kallo ya koma sama: Bidiyon ango ɗan Nigeria sanye da siket yana tiƙa rawa a ranar aurensa ya ɗauki hankula

Bidiyon saurayin da ya bata rai bayan budurwar da ya gayyata cin ‘Pizza’ ta zo da wasu kawayenta biyu
Bidiyon saurayin da ya bata rai bayan budurwar da ya gayyata cin ‘Pizza’ ta zo da wasu kawayenta biyu Hoto: @wisdom_blogg
Source: Instagram

Mutumin ya zuba ido yana kallon pizza da aka bude a gabansa ba tare da ya taba shi ba, kamar wanda ya rasa dandanonsa.

Daya daga cikin matan, wacce ta nadi bidiyon lamarin ta yi dariya yayin da ta ke yi wa mutumin ba'a.

Ga dukkan alamu bai yi tsammanin haka ba.

Kalli bidiyon a kasa:

'Yan Najeriya sun soki yarinyar saboda abin da tayi

@ozirigeorge ya ce:

"Yarinyar da ke daukar bidiyon mayya ce ji wani irin dariya dan Allah mutumin nan na tafasa ne a ciki amma ba zai iya fadi ba. Choi! E choke."

@official_ybizzy ya ce:

"Idan na biya saboda ya riga ya faru to za ta ci gaba da zama a gidana har zuwa mako guda. Za ta gyara ko'ina ta yi girki."

Read also

Tunde Bakare ya yi magana game da shirin takarar 2023 bayan ya sa labule da Buhari

@oliveroky ya rubuta:

"Na tuna da wanda na gayyata a lokacin NYSC ita kuma ta kawo 'yar uwarta. Na bata rai. Na siya mata da kaina, ba ' yar uwarta ba. 'Yar uwar ma gata da fadin rai. Smh."

Matar da ta siya wa mijinta mota ta ce za ta iya siya masa jirgin sama idan tana da hali

A wani labarin, wata ‘yar Najeriya Gbadewole Olubunmi Mary da ta bai wa mijinta kyautar sabuwar mota kirar Mercedes Benz a ranar zagayowar ranar aurensu na 7, ta ce za ta so yi masa kyautar jirgin sama idan Allah ya albarkace ta.

Da take magana da @bbcnewsyoruba, matar ta ce ta saya wa mijinta motar ne saboda shi mutum ne mai kyauta.

A cewar Mary, mutane ba sa ba mijinta kyaututtuka duk da cewa shi mutum ne mai bayarwa. Ta ce tana ta tunanin baiwa mutumin wani babban kyauta tun lokacin da suka haifi dan su na farko.

Read also

Ku ba 'yan bindiga hadin kai don tsira da rayukanku, shawarin 'yan sanda ga 'yan Najeriya

Source: Legit.ng

Online view pixel