Majalisa ta tabbatar da nadin Justis Baba Yusuf a matsayin alkalin kotun birnin tarayya

Majalisa ta tabbatar da nadin Justis Baba Yusuf a matsayin alkalin kotun birnin tarayya

  • An tabbatar da nadin Justis Husseini Yusuf a matsayin babban alkalin babbar kotun birnin tarayya
  • Yan majalisar dattawan Najeriya ne suka tabbatar da nadin alkalin a ranar Talata, 12 ga watan Oktoba
  • An tabbatar da nadin Yusuf ne bayan kwamitin majalisar dattawa kan al’amuran shari’a ta gabatar da rahoton ta

FCT, Abuja - Majalisar dattawan Najeriya a ranar Talata, 12 ga watan Oktoba ta tabbatar da nadin Mai shari’a Husseini Baba Yusuf a matsayin babban alkalin babbar kotun birnin tarayya.

Tabbatarwar Justis Yusuf na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin shugaban majalisar dattawa, Ezrel Tabiowo ya fitar.

Majalisa ta tabbatar da nadin Justis Baba Yusuf a matsayin alkalin kotun birnin tarayya
Majalisa ta tabbatar da nadin Justis Baba Yusuf a matsayin alkalin kotun birnin tarayya Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Rahoto daga kwamitin majalisar dattawa kan alkalin

Tabiowo ya ce an tabbatar da alkalin ne biyo bayan duba rahoton da kwamitin kula da harkokin shari’a, kare hakkin dan adam da al’amuran shari’a suka gabatar.

Kara karanta wannan

Sakin Nnamdi Kanu zai kawo ƙarshen rashin tsaro a kudu maso gabas, Sanata Ubah

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake gabatar da jawabi a zauren majalisar, shugaban kwamitin, Sanata Michael Bamidele, ya ce nadin Yusuf da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi ya cika bukatun Kundin Tsarin Mulkin 1999.

Sanatan ya ce nadin nasa ya yi daidai da Dokokin majalisar Dattawa na 2015, kamar yadda aka yi kwaskwarima.

Kwarewar Justice Yusuf a matsayin alkali

Da yake bayyana sabon alkalin babban kotun na FCT a matsayin gogaggen alkalin Najeriya wanda ke da gogewa sosai, sanatan ya ce Yusuf yana da kyawawan halayen jagoranci na jami'in shari'a.

A cewar Bamidele, sabon alkalin babbar kotun zai yi aiki yadda ya kamata cikin girma.

Ya ce sabon babban alkalin wanda aka nada a matsayin mukaddashin shugaban kotun a ranar 1 ga Agusta, 2021, ya rike mukaminsa har zuwa lokacin da shugaban kasa ya nada shi a kwanan nan.

Kara karanta wannan

Kasafin kudin 2022 da Buhari ya ba majalisa ya tsallake caccaka a zama na biyu

Ya kara da cewa har zuwa lokacin da aka tabbatar da shi, babu wani korafi ko kara da aka gabatar kan sabon babban alkalin kuma bincike da hukumomin tsaro suka gudanar sun kasance nagari.

Buhari ya nada Justis Hussein Baba-Yusuf a matsayin Babban Alkalin Birnin Tarayya

A baya mun kawo cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, 5 ga watan Oktoba, ya nemi Majalisar Dattawa da ta tabbatar da Mai Shari’a Hussein Baba-Yusuf a matsayin Babban Alkalin Babban Birnin Tarayya (FCT).

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan ne ya karanto wasikar shugaban kasar a zauren majalisar a yayin zamansu na yau, jaridar The Nation ta ruwaito.

Buhari a ranar 14 ga watan Agusta ya nada Justice Baba-Yusuf a matsayin mukaddashin babban alkalin babban birnin tarayya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel