Kasafin kudin 2022 da Buhari ya ba majalisa ya tsallake caccaka a zama na biyu

Kasafin kudin 2022 da Buhari ya ba majalisa ya tsallake caccaka a zama na biyu

  • Kwanaki bayan da shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2022, batun ya wuce zama na biyu a majalisa
  • A makon jiya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudi ga gamayyar majalisar dokokin kasar
  • Kasafin kudin, ya bayyana adadin kudaden da ake bukata don cimma ayyukan da gwamnati ta tsara a shekarar ta 2022

Jaridar TheCable ta ruwaito cewa, takardun kasafin kudi na 2022 sun wuce karatu na biyu a majalisar dattawa.

Majalisar dattawan ta zartar da kasafin kudin ranar Laraba 13 ga watan Oktoba bayan muhawara kan manyan ka'idojin ta na tsawon kwanaki biyu.

Da yake ba da gudummawa ga muhawarar, Enyinnaya Abaribe, shugaban marasa rinjaye na majalisar dattijai, ya ce akwai bukatar gwamnatin tarayya ta dakile abin da ya bayyana a matsayin "cin bashi".

Read also

Kasafin kudi: Naira Biliyan 134 sun yi mana kadan inji ‘Yan Majalisar Najeriya

Shugaban marasa rinjaye ya ce ya kamata Babban Bankin Najeriya (CBN) ya tsaya kan aikinsa na sarrafa tattalin arzikin kasar.

Kasafin kudin da shugaba Buhari ya ba majalisa ya zarce zama na biyu
Shugaba Buhari yayin gabatar da kasafin kudi | Hoto: Buhari Sallau
Source: UGC

Wasu sanatoci da dama sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kara gudanar da ayyukan gine-gine a fadin kasar nan.

Da yake jawabi a karshen muhawara kan kasafin kudin, Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya ce rance ba laifi bane muddin ana amfani da shi ga abin da aka ware don shi.

Shugaban majalisar dattawa ya ce ya kamata majalisar kasa ta iya kammala zartar da kasafin kafin watan Disamba.

A makon da ya gabata, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudi na naira tiriliyan 16.39 ga wani zaman gamayyar majalisar dokokin kasar.

A cikin kasafin, gwamnatin Buhari ta ware makudan kudaden da suka kai Naira miliyan 650 don fara aikin wutar Mambila, kudin da ya yi kasa da biliyan daya, inji rahoton Daily Trust.

Read also

Kasafin kudin 2022 ya wuce karatu na biyu a majalisar wakilai

Tsohon Jigon APC yace ‘Yan Najeriya su shiryawa bakar wahala bayan ganin kasafin 2022

A wani labarin, Tsohon mataimakin sakataren yada labarai na jam’iyyar APC na kasa, Timi Frank, ya yi kira ga al’ummar Najeriya su shirya fuskantar kalubale.

This Day ta rahoto Kwamred Timi Frank yana wannan jawabin a matsayin martani ga kasafin kudin shekarar 2022 da shugaban Najeriya ya gabatar.

Timi Frank yace abin da yake shiga aljihunan mutane ya ragu, sannan fetur da wuta za su kara tsada, baya ga wasu haraji da gwamnati za ta shigo da su.

Source: Legit

Online view pixel