Yanzu-yanzu: Yan takara 15 sun kai kara, Kotu ta cire sabon Sarkin Sudan na Kontagora

Yanzu-yanzu: Yan takara 15 sun kai kara, Kotu ta cire sabon Sarkin Sudan na Kontagora

  • Zaben Sabon Sarkin Kontagora ya bar baya da kura
  • Yarimomi 15 sun kai kara kotu kan zargin rashin adalci da magudi
  • Gwamnan jihar ya zabi Mohammad Barau matsayin sabon Sarkin Sudan

Wata babbar kotu dake zamanta a Minna, birnin jihar Neja a ranar Talata ta umurci Mohammed Barau Kontagora ya daina kiran kansa sabon Sarkin Sudan na Kontagora.

Wannan umurni ya biyo bayan karar ex-parte da wasu Yarimomi 15 suka shigar kotun.

Wadanda aka kai kara sune Sabon Sarkin , Mohammed Barau Kontagora, Antoni Janar na jihar Neja, Kwamishanan kananan hukumomi da masarautun gargajiya.

Alkali Abdullahi Mikailu ya umurci Mohammed Barau Kontagora ya daina kiran kansa Sarkin Kontagora "har sai bayan kammala shari'a kan karar da aka shigar ranar 11/10/2021.”

Read also

Jerin matasan Najeriya 6 da suka hau kujerun gwamnoni, sun dauki tsauraran matakai

An dage zaman kotun zuwa ranar 20 ga Oktoba, 2021.

Yanzu-yanzu: Yan takara 15 sun kai kara, Kotu ta cire sabon Sarkin Sudan na Kontagora
Yanzu-yanzu: Yan takara 15 sun kai kara, Kotu ta cire sabon Sarkin Sudan na Kontagora
Source: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan tirka-tirka, an zabi Mohammad Barau matsayin sabon Sarkin Kontagora

Bayan tirka-tirka da rikice-rikice a Masarautar Kontagora, an sanar da Muhammad Barau Kontagora a matsayin sabon Sarkin Sudan na Kontagora.

Kwamishanan kananan hukumomi da lamuran masarautun gargajiya, Emmanuel Umar, ya bayyana hakan a jawabin da sakataren yada labaran gwamnan, Mary Berge ta saki ranar Laraba.

A baya Gwamnan jihar Neja, Abubakar Bello, ya yi watsi da nadin sabon Sarkin Kontagora, bisa karar da wasu yan takara 46 suka shigar kan zargin murdiya da rufa-rufa da akayi a zaben.

Hakazalika gwamnan ya canza kwamishanan harkokin sarakunan gargajiya. Abdulmalim Sarkin-Daji, wanda ake zargi da murdiyan, rahoton Premium Times.

A ranar Lahadi, an sanar da babban dan kasuwa Mohammadu Barau-Mu’azu, matsayin sabon Sarkin Kontagora, bayan samun rinjaye a zaben da masu zaben Sarki biyar suka kada.

Read also

Siyasar Kano: Jerin Jiga-jigan APC 10 da suka kai karar Gwamna Ganduje wajen uwar Jam’iyya

Source: Legit

Online view pixel