Yanzu-yanzu: Bayan tirka-tirka, an zabi Mohammad Barau matsayin sabon Sarkin Kontagora

Yanzu-yanzu: Bayan tirka-tirka, an zabi Mohammad Barau matsayin sabon Sarkin Kontagora

  • eDaga karshe, an zabi sabon Sarkin Sudan na masarautar Kontagora a jihar Neja
  • Gwamnan Jihar ya amince da zabin farko da akayi a zaben watan Satumba
  • Sama da Yarimomi 45 suka nemi kujerar sarautar Sarkin Sudan

Neja - Bayan tirka-tirka da rikice-rikice a Masarautar Kontagora, an sanar da Muhammad Barau Kontagora a matsayin sabon Sarkin Sudan na Kontagora.

Kwamishanan kananan hukumomi da lamuran masarautun gargajiya, Emmanuel Umar, ya bayyana hakan a jawabin da sakataren yada labaran gwamnan, Mary Berge ta saki ranar Laraba.

Kwamishanan ya bayyana cewa lallai zaben da akayi tun farko ya bi ka'ida kuma gwamnan jihar ya rattafa hannu.

Umar yace:

"Zaku tuna cewa an yi zaben Sarkin Sudan na Kontagora ranar Lahadi, 19 ga Satumba. Amma wasu yan takara suka kai kara wajen gwamnan Neja cewa an yi magudi."

Read also

Yanzu-Yanzu: Manyan PDP sun amince dan arewa ya shugabanci jam'iyyar

"Sakamakon haka gwamnan ya gana da kwamitin zaben sarkin kuma ya tuntubi majalisar masu sarautar gargajiya a jihar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Emmanuel Umar ya kara da cewa tattaunawarsu da gwamnan, kwamitin nadin sarkin sun bayyana cewa anyi zaben bisa ka'ida da al'adar masarautar Kontagora kuma ba'ayi magudi ba.

Yace:

"Saboda haka gwamnan ya amince da nadin Mohammed Barau Kontagora matsayin Sarkin Sudan na 7 na Masarautar Kontagora."

Bayan tirka-tirka, an zabi Mohammad Barau matsayin sabon Sarkin Kontagora
Yanzu-yanzu: Bayan tirka-tirka, an zabi Mohammad Barau matsayin sabon Sarkin Kontagora Hoto: Mary Noel-Berje
Source: Facebook

Gwamnan Neja ya dakatad da zaben sabon Sarkin Kontagoran kan zargin murdiya

A baya Gwamnan jihar Neja, Abubakar Bello, ya yi watsi da nadin sabon Sarkin Kontagora, bisa karar da wasu yan takara 46 suka shigar kan zargin murdiya da rufa-rufa da akayi a zaben.

Hakazalika gwamnan ya canza kwamishanan harkokin sarakunan gargajiya. Abdulmalim Sarkin-Daji, wanda ake zargi da murdiyan, rahoton Premium Times.

A ranar Lahadi, an sanar da babban dan kasuwa Mohammadu Barau-Mu’azu, matsayin sabon Sarkin Kontagora, bayan samun rinjaye a zaben da masu zaben Sarki biyar suka kada.

Read also

An tattauna da 'yan bindiga a Zamfara, sun sako mutane sama da 200

Amma daga sanarwar, sauran yan takara suka fara zanga-zanga inda suka zargi Kwamishana Sarkin-Daji da rufa-rufa.

Sun ce ba'ayi daidato wajen zaben ba saboda Kwamishanan na da wanda yake so.

Source: Legit

Online view pixel