Yanzu-Yanzu: Matasa a Sokoto suna can suna zanga-zanga kan rashin tsaro, suna ƙone-ƙone

Yanzu-Yanzu: Matasa a Sokoto suna can suna zanga-zanga kan rashin tsaro, suna ƙone-ƙone

  • Matasa sun fito zanga-zanga a kan titunan garin Goronyo da ke jihar Sokoto
  • Sun yi zanga-zangar ne domin neman gwamnati ta kawo musu dauki kan batun rashin tsaro
  • Yawan hare-haren 'yan bindiga yana tilastawa mazauna garin yin hijira zuwa wasu garuruwan

Sokoto - Wasu matasa a garin Goronyo da ke karamar hukumar Goronyo a jihar Sokoto sun fito kwansu da kwarkwata a tituna suna zanga-zangar halin rashin tsaro da yankinsu ke ciki.

SaharaReporters ta ruwaito cewa suna can suna zanga-zangar a lokacin hada wannan rahoton.

Yanzu-Yanzu: Matasa a Sokoto suna can suna zanga-zanga kan rashin tsaro, suna kone-kone
Matasa a Sokoto suna can suna zanga-zanga kan rashin tsaro, suna kone-kone. Hoto: SaharaReporters
Asali: Facebook

Wani majiya ya ce matasan sun fito zanga-zangar ne saboda kallubalen tsaro a yankin, wadda ya tilastawa mutane da dama tserewa daga garin.

Kara karanta wannan

Kaduna: Jami'an tsaro sun halaka 'yan bindiga 10 a Giwa, sun ceci mutum 1

Ya ce:

"Ana yin zanga-zanga a garin Goronyo da ke jihar Sokoto. Matasa sun cika tituna suna nuna damuwarsu kan rashin tsaro da ya tilastawa mutane yin hijira barin garin. Suna can suna zanga-zangar a yanzu."

Hotunan da SaharaReporters ta samu sun nuna an kafa shinge a kan tituna, matasan kuma na kona tayoyi domin nuna rashin jin dadinsu game da kashe-kashe da garkuwa da mutane a yankin.

Sokoto na daya daga cikin jihohin Arewa da ke fama da matsalar 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

A baya-bayan nan gwamnatin jihar ta bada umurnin a toshe layukan sadarwa a wasu yankunan jihar don dakile hare-haren 'yan bindigan.

Toshe layukan sadarwar ya shafi kananan hukumomi kamar Dange Shuni, Tambuwal, Sabon Birni, Raba, Tureta, Goronyo, Tangaza da sauransu.

Sokoto: Yadda ƴan bindiga suka amshe miliyoyi daga basarake kuma suka ƙi sako waɗanda suka yi garkuwa da su

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun kai hari ofishin yan sanda, sun saki wadanda aka tsare sun kona motocin sintiri

A wani rahoto daga Sokoto, 'Yan bindiga sun amshe Naira miliyan 2.2 (N2,200,000) a matsayin kudin fansa amma sun ki sakin mutane 20 da su ka sata.

Buzu, na biyu a hatsabibanci daga Bello Turji, duk da an biya shi makudan kudade don sakin mutane 20 da su ka sata a Gatawa ya murje ido ya lamushe kudin babu wani bayani.

Premium Times ta ruwaito yadda ‘yan bindigan su ka aika wa dagacin Burkusuma da sarkin Rafi wasika inda su ka bayyana cewa su na bukatar N20,000,000 a matsayin kudin fansar wadanda su ka sata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164