Yanzu-Yanzu: Majalisa ta saduda, ta bawa INEC wuka da nama kan batun tura sakamakon zabe

Yanzu-Yanzu: Majalisa ta saduda, ta bawa INEC wuka da nama kan batun tura sakamakon zabe

  • Majalisar dattawar Nigeria ta bawa hukumar INEC ikon zaben tsarin da za ta yi amfani da shi wurin taro sakamakon zabe
  • Hakan ya biyo bayan mahawarra da aka dade ana yi kan turo zabe ta intanet ko kuma da takarda a rubuce kamar yadda ake yi a baya
  • A sauye-sauayen da majalisar ta yi wa dokar zaben, ta kuma wajabtawa jam'iyyun siyasa amfani da tsarin kato-bayan-kato yayin zaben cikin gida

Abuja - Majalisar dattawar Nigeria ta sake duba kudirin yi wa dokar zabe garambawul da bawa hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, damar zaben hanyar da ta fi dacewa don tura sakamakon zabe.

A ruwaiyar ta The Cable, yanzu hukumar zaben tana da damar zaben hanyar da za ta yi amfani da shi wurin tura sakamakon zaben - ko ta yanar gizo wato intanet ko kuma da takarda da biro.

Kara karanta wannan

NAF ta karyata rahoton biyan 'yan bindiga N20m don kada su harbo jirgin Buhari

Yanzu-Yanzu: Majalisa ta saduda, ta bawa INEC wuka da nama kan batun tura sakamakon zabe
Yanzu-Yanzu: Majalisa ta saduda, ta bawa INEC wuka da nama kan batun tura sakamakon zabe
Asali: Original

Har wa yau, majalisar ta kuma amince da cewa dukkan jam'iyyun siyasa su yi amfani da tsarin kato-bayan-kato wurin zaben 'yan takararsu yayin zaben cikin gida.

Majalisar ta kuma amince da wasu sakin layuka hudu cikin kudirin neman yi wa dokar zaben garambawul.

A watan Yuli, Majalisa ta bawa hukumar sadarwa ta kasa, NCC, damar tura sakamakon zabe ta hanyar yanar gizo.

Hakan ya janyo cece-kuce inda wasu da dama suka rika kira ga majalisar dattawa ta yi koyi da majalisar wakilai na tarayya da suka amince a yi amfani da fasahar zamanin 'a wuraren da hakan zai yi wu'.

Yayin da ya ke gabatar da kudirin a farkon zaman a ranar Talata, Yahaya Abdullahi, ya ce akwai bukatar yin garambawul a kan kudirin.

Kara karanta wannan

A tura matasan NYSC faggen yaki da yan bindiga, wanda ba zai je ba a daina biyansa albashi

Ya ce:

"Bayan yin nazari kan kudirin da kwamitin majalisa na INEC ta yi, an ga akwai bukatar yin garambawul a wasu sassa kamar 43, 52, 63 da 87."
"Don haka kwamitin ta yi wasu gyare-gyare tana mai dogaro da oda na 1(b) da 53(b)."

Da ya ke tofa albarkacin bakinsa, Enyinnaya Abaribe yace a bar jam'yyun siyasa su zabi tsarin da suke so wurin zaben fidda gwani yana mai cewa ba dukkanin jam'iyyu ke iya yin kato-bayan-kato ba.

A bangarensa, Opeymi Bamidele daga Ekiti Central ya ce tilasta amfani da kato-bayan-kato din zai tabbata kowanne dan jam'iyya ya shiga an dama da shi.

Bamidele ya ce:

"Kan batun zaben cikin gida, an yi hakan ne don tabbatar kowanne mamba ya shiga an dama da shi.
"Wani hanya ce na mayarwa al'umma iko a hannunsu".

Saurari cikaken rahoton ...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164