Na Cika Alkawuran Da Na Yiwa Yan Najeriya Cikin Shekaru 7, Buhari

Na Cika Alkawuran Da Na Yiwa Yan Najeriya Cikin Shekaru 7, Buhari

  • Shugaba Buhari ya bayyana irin nasarorin da gwamnatin ta samu cikin shekaru bakwai da yayi kan mulki
  • Buhari yace daga cikin kokarin da yayi an yiwa yan Najeriyan 38.7 million rigakafin cutar Korona
  • Saura watanni takwas yanzu gwamnatin shugaba Muhammadu ta cika shekaru takwas

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci taron waiwaye kan ayyukan da Ministocinsa sukayi cikin shekaru 7 da suka gabata tun da ya hau mulki.

Buhari ya bayyana cewa lallai ko shakka babu ya cika dukkan alkawuran da ya yiwa al'ummar Najeriya.

Taron ya samu halartan tsohon shugaban kasar Kenya, Uhurru Kenyatta, rahoton Leadership.

Shugaban kasan ya bayyana irin nasarorin da ya samu a bangaren aikin noma, gine-gine, tsaro, kiwon lafiya, yaki da rashawa, dss.

Kara karanta wannan

Saura Wata 7 a Bar Ofis, Buhari Ya Fadawa Ministoci Su Fara Shirye-Shiryen Mika Mulki

Buhari ya bayyana cewa ya gina sabbin tituna sama da kilomita 3800, ya sayawa hukumar sojin saman Najeriya sabbin jirage 38 don yaki da yan bindiga.

Ya kara da cewa daga cikin nasarorinsa shine baiwa yan Najeriya 38.7 million rigakafin Korona.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Buhari
Na Cika Alkawuran Da Na Yiwa Yan Najeriya Cikin Shekaru 7, Buhari Hoto; Buhari
Asali: Depositphotos

Buhari yace:

"Game da ginin Tituna, gwamnatin nan ta gina titunan kilomita 408m, 2,499km na SUKUK kuma na gyara tituna 15,961Km a fadin tarayya."
"Na dauki sabbin yan sanda 20,000"
"Hukumar Sojin Sama ta syai sabbin jirage 38 kuma mun yi odan sabbi 36, yayinda hukumar sojin ruwa ta sayi sabbin jiragen ruwa na yaki, Seaward Defence, Whaler , da jirage masu saukan angulu."

Game da kula da al'umma kuwa, shugaban kasa ya cewa yanzu haka ana ciyar da daliban firamare 9,990,862 kuma an dauki masu girki 128,531.

Game da yaki da rashawa, Buhari ya yi alkawarin cewa zasu cigaba da hukunta dukkan wadanda aka kama suna rashawa da almundahana.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya Ba Zasu Fahimci Alherin Buhari Ba Sai Daga Baya, Tinubu

Yan Najeriya Ba Zasu Fahimci Alherin Buhari Ba Sai Daga Baya, Tinubu

Dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, Bola Tinubu, a ranar Talata ya jinjinawa shugaba Muhammadu Buhari bisa kokarin da ya yiwa al'ummar Najeriya.

Tinubu ya ce Buhari ya kwantar da hankalinsa, da sannu yan Najeriya zasu fahimci darajarsa.

Tinubu ya bayyana hakan a jawabin da yayi na fatan alheri ga Buhari a taron bitar ayyukan Ministoci da Sakatarorin din-din-din dake gudana a Abuja

Asali: Legit.ng

Online view pixel