Bayan komawa Jam'iyyar APC, Gwamnan Arewa ya rantsar da sabbin kwamishinoni, SSG da masu bashi shawara
- A karon farko bayan zama cikakken ɗan jam'iyyar APC, Gwamna Matawalle ya rantsar da sabbin kwamishinoni da masu ba shi shawara
- Gwamnan na jihar Zamfara ya kuma bada rantsuwar kama aiki ga sabon sakataren gwamnati da kuma shugaban ma'aikata
- Ya gargaɗe su cewa gwamnatinsa ba zata lamurci duk wani lalaci da sakaci ba musamman a dai-dai lokacin da ta maida hankali kan yan bindiga
Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya rantsar da sabbin yan majalisar zartarwarsa da sakatarorin dindindin a jihar, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
Mai taimakawa gwamnan ta ɓangaren yaɗa labarai, Zailani Bappa, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.
Kabiru Balarabe da Kabiru Mohammed, sun karɓi rantsuwar fara aiki a matsayin sakataren gwamnatin jiha da kuma shugaban ma'aikata.
Hakanan kuma, gwamna Matawalle ya bada rantsuwar kama aiki ga sabbin kwamishinoni 18 da masu bada shawara ta musamman 11.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Legit.ng Hausa ta gano cewa gwamnan ya rantsar da sabbin mataimakan nasa ne bayan sun rantse da Allah basu da hannu kwata-kwata a matsalar yan bindiga da ta addabi jihar.
Sabuwar gwamnati zamu kafa - Matawalle
A jawabinsa, Gwamna Matawalle, ya yi kira ga sabbin mataimakansa da su yi aiki tukuru a abinda ya kira da "Sabon farko" bayan cimma nasarori a shekaru biyu da suka shuɗe.
A rahoton Daily Nigerian, Gwamna Matawalle yace:
"Idan ka duba nagartar sabbin mambobind a muka rantsar a sabuwar tawagar gwamnatin mu, ya isa kowa ya fahinci cewa sabuwar tafiyar gyara Zamfara yanzu ta fara."
Ba zan lamurci sakaci da holewa ba
Matawalle ya kuma gargadi mutanen da ya naɗa cewa gwamnatinsa ba zata lamurci sakaci da holewa ba musamman a lokacin da ake kokarin kawo karshen ayyukan yan bindiga.
Ya kuma ƙara da cewa an samu nasarori da dama sakamakon tsauraran matakan da gwamnati ta ɗauka kwanan nan domin dakile yan ta'adda a jihar Zamfara.
A wani labarin na daban kunji cewa Dubun masu garkuwa da mutane, yan leken asiri da masu kaiwa yan bindiga kayan abinci ya cika a jihar Sokoto
Jami'an tsaro sun samu nasarar cafke masu garkuwa da mutane 11, yan leken asiri da kuma masu jigilar kaiwa yan bindiga abinci a Sokoto.
Hukumar NSCDC ta bayyana cewa mutanen da ake zargin suna aikinsu ne a yankunan Tureta da Dange/Shuni.
Asali: Legit.ng