Yadda gwamnan Kano Ganduje ya mika wa 'yar shekaru 14 mulkinsa na dan lokaci

Yadda gwamnan Kano Ganduje ya mika wa 'yar shekaru 14 mulkinsa na dan lokaci

  • Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ba wata yarinya kujerarsa na mintuna 20
  • Wannan na zuwa ne a ranar 'ya mace ta duniya, ranar da ake murnar ta a ranar 11 ga watan Oktoba duk shekara
  • Mutane sun yi martani, tare da bayyana ra'ayoyinsu kan abin da gwamnan ya yi da kuma abin da yarinyar ta ji

A wani bangare na shagalin murnar ranar 'ya mace ta Duniya, Gwamna Kano, Abdullahi Ganduje ya mika mukaminsa ga Atika Abubakar Yankaba mai shekaru 14 na tsawon mintuna 20.

Atika, wacce daliba ce ta karamar sakandare aji 3, ta hau ofis da misalin karfe 12 na rana sannan aka mayar wa Gwamna Ganduje da karfe 12:20 na rana.

Read also

Buhari ya ce gwamnatinsa ta shirya za ta fara kera makamai saboda wasu dalilai

@Bbcnewspidgin ta yada wani hoton matashiyar a shafin Instagram. A cikin hoton, ana iya ganin yarinyar tana murmushi yayin da ta ke zauna a kujerar gwamna.

Yadda gwamnan Kano Ganduje ya mika wa 'yar shekaru 14 mulkinsa na dan lokaci
Gwamna Ganduje ya daura yarinya 'yar shekaru 14 a kujerarsa | Hoto: @govumarganduje, @bbcnewspidgin
Source: Instagram

Ranar 'ya mace ta Duniya rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana, wacce aka fara murnar ta a ranar 11 ga Oktoba, 2012.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sharhin jama'a kafar Instagram

Jama'a da yawa masu amfani da Instagram sun mamaye sashin sharhi don bayyana ra'ayoyinsu kan wannan hoto da kuma abin da gwamnan ya yi.

@emmanuelparatodo ya ce:

"To me ta cimma da zama gwamna na mintuna 20."

@abigail_nathaniel tayi sharhi da cewa:

"Kada ku damu da su, ba za su taba tallafa wa mata su samu mulki a matsayin gwamna ko shugaban kasa a Najeriya ba, suna yaudarar mu ne kawai."

@chisomottah ya rubuta:

"Minti 20, kawai a zauna a yi murmushi. Mai girma gwamnan zama da murmushi."

Read also

Hotunan Zulum tare da mazauna kauyen Banki yayin da suke cin kasuwar dare

@lomton01 ya ce:

"Idan Buhari ya gwada wannan hadarin."

@osascoyo yayi sharhi:

"Ta yi amfani da lokacin don yin abin da ya dace.?"

Labarin gimbiyar da ta bar masarautarsu ta auri talaka ya dauki hankalin jama'a

A wani labarin kuwa, Aljazeera ta ruwaito cewa za a daura auren gimbiya Mako ta kasar Japan da wani talaka mai suna Kei Komuro a watan Oktoba na 2021.

A baya kada, an lura cewa ma'auratan sun yi ta yawo a kafafen yanar gizo kwanaki da suka gabata bayan dangantakar su ta zama sananniya ga jama'a.

Domin ta auri mutumin da kowa yasan gama-gari ne kuma talaka, gimbiyar za ta ba da matsayin sarauta da gadon ta da ya kai biliyoyin kudade.

Source: Legit.ng News

Online view pixel