Gangamin taron APC na Jihohi: Gwamna Ganduje ya kafa sabon sharaɗi ga yan takara a jihar Kano

Gangamin taron APC na Jihohi: Gwamna Ganduje ya kafa sabon sharaɗi ga yan takara a jihar Kano

  • Gwamnatin jihar Kano ta umarci dukkan yan takarar wata kujera a zaɓen shugabannin APC a jihar Kano su je gwajin kwaya
  • Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Muhammad Garba, yace duk wanda ka gani a cikin gwamnatin jihar sai da aka masa wannan gwajin
  • Kwamishinan yace yayin zaɓen shugabannin kananan hukumomi, sai da aka dakatar da yan takarar kansila 13

Kano - Gwamnatin Ganduje tace duk wani mamban jam'iyyar APC dake neman wani mukamin jam'iyya sai ya yi gwajin shan miyagun kwayoyi.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Muhammad Garba, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Jam'iyyar APC ta ƙasa ta shirya gudanar da gangamin taronta na jihohi wanda za'a zaɓi shugabanni a matakin jiha ranar 16 ga watan Oktoba.

Read also

Wata Sabuwa: Matan jam'iyyar PDP Sun bukaci a basu kujerar mataimakin shugaba

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje
Gangamin taron APC na Jihohi: Gwamna Ganduje ya kafa sabon sharaɗi ga yan takara a jihar Kano Hoto: dailynigerian.com
Source: UGC

Kwamishinan ya shawarci dukkan yan takara da su je ofishin hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ranar Talata da misalin ƙarfe 7:00 na safe.

Shin gwamnatin Kano ta yi haka a tarukan baya?

Bugu da ƙari, Kwamishina yace sai da aka gudanar da makamancin irin wannan gwajin ga yan takara a zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi.

Hakanan sai da aka yiwa duk wani mai rike da mukamin siyasa na jiha, da ya haɗa da mambobin kwamitin zartarwa na jihar Kano, kafin a basu ofishinsu.

Garba ya ƙara da cewa tuni gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, ya sanar da hukumar NDLEA ta gudanar da gwajin.

Ya kuma yi gargaɗin cewa gwamnati zata ɗauki mataki kan duk wanda ta gano yana ma'amala da wasu haramtattun kwayoyi kuma ba kan ƙa'ida ba.

Read also

Da Duminsa: Jam'iyyar APC ta dakatar da gangamin taronta a wannan jihar

Shin yin wannan gwajin zai amfanar da wani abu?

Garba yace yayin zaɓen shugabanni a matakin ƙananan hukumomi, aƙalla yan takarar kansila 13 aka dakatar, kuma aka maye su da wasu bayan gwajin NDLEA ya bayyana suna ma'amala da kwayoyi.

Leadership ta rahoto kwamishina yace:

"Wannan gwamnatin ta shirya sosai wajen yaƙi da safarar miyagun kwayoyi da kuma amfani da kwaya ba bisa ƙa'ida ba."

A wani labarin na daban kuma Gwamnan PDP ya gama shirin sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki, PDP ta maida martani

Babbar jam'iyyar hamayya PDP ta ƙaryata labarin da ake yaɗawa cewa gwamnan Akwa Ibom, Udom Emmanuel, zai koma APC.

Babban mai baiwa shugaba Buhari shawara ta musamman kan harkokin Neja Delta, Sanata Enang, shine ya fara ikirarin komawar gwamnan APC.

Source: Legit

Online view pixel