Gwamnan PDP ya gama shirin sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki, PDP ta maida martani

Gwamnan PDP ya gama shirin sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki, PDP ta maida martani

  • Babbar jam'iyyar hamayya PDP ta ƙaryata labarin da ake yaɗawa cewa gwamnan Akwa Ibom, Udom Emmanuel, zai koma APC
  • Babban mai baiwa shugaba Buhari shawara ta musamman kan harkokin Neja Delta, Sanata Enang, shine ya fara ikirarin komawar gwamnan APC
  • Amma PDP reshen jihar ta fito ta bayyana cewa sam babu wannan maganar a ƙasa, babu inda gwamna zai je

Akwa Ibom - Jam'iyyar PDP reshen jihar Akwa Ibom, ta yi watsi da jita-jitar cewa gwamna Udom Emmanuel ya kammala shirye-shiryen sauya sheƙa zuwa APC.

Jaridar Punch ta rahoto PDP na cewa mutane na amfani da wannan jita-jitar ta ƙarya ne domin ɗauke hankalin wasu zuwa gare su.

Babban mai taimakawa shugaban Buhari kan harkokin Neja Delta, Sanata Ita Enang, ya bayyana cewa gwamnan ya nuna wasu alamun zai koma APC.

Read also

Babban dalilin da yasa yan Najeriya ba zasu amince da Igbo ya zama shugaban ƙasa a 2023 ba, Dokpesi

Gwamna Udom Emmanuel
Gwamnan PDP ya gama shirin sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki, PDP ta maida martani Hoto: vanguardngr.com
Source: UGC

Wane alamu gwamnan ya nuna?

Sanata Enang ya faɗi alamun da yasa ya faɗi haka, waɗanda suka haɗa da ganawa da manyan jiga-jigan APC da gwamnan ya yi kwanaki kaɗan baya.

Daga cikin jiga-jigan APC ɗin akwai, mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, da shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan, waɗanda suka ziyarci jihar Akwa Ibom domin kaddamar da wasu ayyuka.

Enang yana ganin hakan da gwamna Udom Emmanuel, ya yi ya nuna ƙarara cewa ya zama mamba a jam'iyyar APC, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

PDP ta maida martani

Da yake martani kan ikirarin sanata Enang, kakakin jam'iyyar PDP na jihar, Mr. Borono Bassey, yace sam bai yi mamakin yaɗa irin wannan jita-jitar ba.

Ya ƙara da cewa a koda yaushe APC tana faɗi tashin samun haziƙin gwamna kamar Udom Emmanuel, domin ta ɓoye gazawarta a jihar.

Read also

Da Dumi-Dumi: Mambobin Jam'iyyun Hamayya Sama da 5,000 Sun Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar APC

Yace:

"Maganar gaskiya gwamna da kanshi ya faɗa kuma ya sake nanatawa kuma mu a jam'iyya mun bayyana cewa gwamnan mu yana nan daram a PDP."
"Ina tunanin kawai wasu mutane na son janye hankalin al'umma ne, saboda sun fahimci ana son jin irin wannan labarin."

A wani labarin kuma mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, yace farin jinin shugaba Buhari da nagartarsa sun isa magance matsalolin Najeriya

A cewarsa, babu ɗan siyasar Najeriya da ya fi shugaba Buhari ƙaurin suna da nagarta a wannan zamanin da muke ciki.

Osinbajo ya yi kira ga yan Najeriya dake ciki da wajen Najeriya su cigaba da kasancewa tsintsiya ɗaya.

Source: Legit.ng

Online view pixel