Bayan korar ministoci biyu, Buhari ya gargadi ministocinsa kan aiki tukuru

Bayan korar ministoci biyu, Buhari ya gargadi ministocinsa kan aiki tukuru

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargadi ministocinsa da su rike aiki tukuru da amana
  • Ya bayyana cewa, akwai bukatar su jajirce domin gwamnatinsa ta cika alkawuran da ta dauka
  • Ya bayyana haka ne yau Litinin yayin wani taron tattara kwazon ministocin nasa na shekaru biyu

Abuja - Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a ranar Litinin, 11 ga watan Oktoba ya karanto dokar tarzoma ga ministoci a majalisar ministocinsa da sakatarorin dindindin a fadin ma'aikatu.

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa shugaban ya bukaci jami'an da su dauki batutuwan aiwatar da ayyukan da aka dora masu da muhimmanci.

Shugaban ya ce yana da mahimmanci jami'an su sani cewa sauke nauyin ayyukansu da muhimmanci zai taimaka wa gwamnatin yanzu ta cimma burin ta da alkawuran da ta yiwa 'yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Buhari ya ce gwamnatinsa ta shirya za ta fara kera makamai saboda wasu dalilai

Bayan korar ministoci biyu, Buhari ya gargadi ministocinsa kan aikin tukuru
Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Auna kima da kididdiga ga Ma’aikatu da Hukumomi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban ya fadi haka ne a taron bitar ayyukan ministoci na rabin wa'adinsa na kwanaki biyu da aka shirya don tantance ci gaban da gwamnatin shugaba Buhari ke kawowa.

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook ya ce Buhari ya yi wannan jawabi ne yayin da ya ke kaddamar da tsarin gudanar da ayyuka na fifiko na shugaban kasa.

Binciko Nasarar Ministoci da Jami'ai

Ya ce tsarin ya fara aiki tun daga watan Janairun 2020 kuma ya baiwa gwamnati damar bibiyar ayyuka a zahirance tare da samun bayanan da suka dace kuma ake bukata.

Adesina ya ce shugaban ya kuma yi alkawarin zai zauna domin sauraron jimillar kimar ayyukan majalisar ministocinsa da na ma'aikatunsa cikin shekaru biyu da suka gabata.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Buhari ya fara bincikar kwazon ministocinsa yayin da ake rade-radin zai kori wasu

Adesina ya ce:

"Hakanan, Shugaban zai shiga cikin tattaunawa kan mafi kyawun dabarun aiwatar da tsare-tsare, shirye-shirye da ayyukan da za su iya habaka tattalin arziki sosai daga dogaro da kudaden shiga na mai, tare da ci gaban tattalin arzikin da ake samu a halin yanzu."

Duba sanarwar

Fasto ya ce ubangijinsa ya ba shi sako ya ba Buhari kan a daina siyo jiragen yaki

A wani labarin, Shahararren malamin addinin kirista na Adoration Ministry da ke jihar Enugu, Rev. Fr. Ejike Mbaka, ya caccaki shugaban kasa Muhammadu Buhari kan cewa, ya daina siyan jiragen yaki ya dukufa wajen gina karin masana’antu.

A cewar malamin na addinin kirista, sakon da ya fada wa Buhari daga ubangiji ne, PM News ta ruwaito.

Ya shaida wa shugaban cewa jiragen da yake sayowa za a yi amfani da su ne wajen lalata kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.