Allah kadai zai iya daukar rayuwa ta: Tinubu ya gana da mukarrabansa

Allah kadai zai iya daukar rayuwa ta: Tinubu ya gana da mukarrabansa

  • Tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu, ya ce Allah kadai zai iya daukar rayuwarsa kuma a lokacin da ya hukunta
  • Jigon jam'iyyar APC ya sanar da cewa ya samu lafiya a taron da Gwamna Sanwo-Olu ya hada masa a gidan gwamnati
  • Gwamna Sanwo-Olu ya bayyana tsabar farin cikinsa ganin dawowar uba kuma shugabansu lafiya sarai

Legas - Bola Tinubu, jigon jam'iyyar APC, ya ce Allah ne kadai zai iya hukunta lokacin da karshen rayuwarsa zai zo.

Tsohon gwamnan jihar Legas ya dawo Najeriya a ranar Juma'a bayan kwashe watanni da yayi ya na jinya a London sakamakon aikin da aka masa a guiwa, TheCable ta ruwaito.

A yayin jawabi a ranar Lahadi yayin da Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas ya shirya masa taron maraba a gidan gwamnatin jihar da ke Ikeja, Tinubu ya ce "ya warke sarai".

Read also

Allah ne mai bada mulki ga wanda ya so kuma a lokacin da ya so, Tinubu ya magantu

Allah kadai zai iya daukar rayuwa ta: Tinubu ya gana da mukarrabansa
Allah kadai zai iya daukar rayuwa ta: Tinubu ya gana da mukarrabansa. Hoto daga thecable.ng
Source: UGC
"A gaskiya da farko na shiga damuwa, amma yanzu ina farin ciki. Allah ne ke bada rayuwa kuma shi kadai zai iya daukar rayuwa," yace.
"Kuma Allah ya ce, idan ya ba ka mulki da dama a rayuwa, shi kadai ke iya kwacewa daga mutum idan bai yi amfani da shi yadda ya dace ba. Allah na iya bada mulki ga duk wanda ya so.
“Ubangiji ne ya ba ni tsayin rayuwa har na kai yau kuma ya ba ni dama. Ina godiya ga Ubangiji saboda ga ni tsaye gaban ku lafiya kalau.
“A yau ranar murna ce. Ga mu muna mika godiya ga Ubangiji. Allah ya yi wa duk wadanda suka halarci wurin nan albarka. Ina godiya kuma ba zan iya cewa komai fiye da haka ba. Nagode."

Read also

'Na warke Sarai', Tinubu ya mika godiya ga wadanda suka masa addu'a

A bangarensa, Sanwo-Olu ya ce wannan lokacin farin ciki ne ga mazauna jihar Legas ganin dawowar Tinubu, TheCable ta wallafa.

"Muna da dalilai masu tarin yawa da ya dace mu mika godiya ga Ubangiji kan dawowar Asiwaju gida cike da lafiya," gwamnan yace.
"Tun ranar Juma'a da shugabanmu kuma babanmu ya dawo, farin ciki ya mamaye mazauna jihar Legas, magoya bayansa da kuma 'yan Najeriya.
“Muna godiya ga Ubangiji da ya dawo mana da shi gida lafiya cike da koshin lafiya."

'Na warke Sarai', Tinubu ya mika godiya ga wadanda suka masa addu'a

A wani labari na daban, Asiwaju Bola Tinubu, jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ya ce ya warware sarai daga jinyar da yayi.

Daily Trust ta ruwaito yadda Tinubu ya kwashe watanni uku a London ya na jinya. An yi masa aiki ne a guiwa kuma zamansa ya sa manyan 'yan siyasa suka dinga zarya zuwa London.

Read also

Labari da Hotuna: Jagoran APC Bola Tinubu ya dawo Najeriya bayan jinya a Landan

A wata takarda da ofishin yada labaransa ya fitar a madadinsa a ranar Juma'a, Tinubu ya ce ya dawo kuma ya "warke sarai sannan zai cigaba da ayyukansa na bunkasa damokaradiyya da mulki na gari a kasar sa."

Source: Legit

Online view pixel