Duk mai sha'awar neman kujerar siyasa ya yi murabus daga mukaminsa, Gwamnan Arewa ga makusantansa

Duk mai sha'awar neman kujerar siyasa ya yi murabus daga mukaminsa, Gwamnan Arewa ga makusantansa

  • Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja, ya umarci yan majalisar gwamnatinsa su aje mukaminsu idan suna neman kujerar siyasa
  • A cewar gwamnan duk wani mai son wani muƙami a APC to wajibi ya aje aikinsa kamar yadda dokokin jam'iyya ya tanazar
  • Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Ahmed Matane, ya fitar ranar Litinin

Niger - Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya umarci masu rike da muƙaman siyasa a gwamnatinsa, waɗanda ke neman wata kujerar jam'iyya, su yi murabus daga mukamansu.

Gwamnan yace duk wanda ke da burin neman wata kujerar siyasa ƙarƙashin jam'iyyar ya gaggauta miƙa takaradar murabus ɗinsa, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Gwamna Abubakar Sani Bello
Duk mai sha'awar tsayawa takara ya yi murabus daga mukaminsa, Gwamnan Arewa ga makusantansa Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Sakataren gwamnatin Neja, Ahmed Matane, shine ya bayyana saƙon gwamnan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Gangamin taron APC na Jihohi: Gwamna Ganduje ya kafa sabon sharaɗi ga yan takara a jihar Kano

Meyasa gwamnatin Neja ta ɗauki wannan matakin?

Sakataren ya ƙara da cewa gwamnati ta ɗauki wannan matakin ne domin yin biyayya ga dokokin jam'iyyar APC mai mulki.

Sanarwa ta ƙara da cewa duk wanda ya yanke hukunci zai iya miƙa takardar murabus dinsa ofishin sakataren gwamnatin jihar nan take.

Dailytrust ta rahoto Wani sashin sanarwar yace:

"Duk mai bukatar neman wata kujera a jam'iyya, to ya gaggauta mika takardar murabus ga ofishin sakataren gwamnati nan take."

Daga ƙarshe, sakataren gwamnatin ya yi fatan duk wanɗanda wannan umarni ya shafa zasu gaggauta yanke hukunci da yin abinda ya dace bada jimawa ba.

A wani labarin na daban kuma kun ji cewa mataimakin shugaban ƙasa yace farin jinin Buhari da nagartarsa zata magance matsalolin Najeriya

Kara karanta wannan

Allah ne mai bada mulki ga wanda ya so kuma a lokacin da ya so, Tinubu ya magantu

A cewarsa, babu ɗan siyasar Najeriya da ya fi shugaba Buhari ƙaurin suna da nagarta a wannan zamanin da muke ciki.

Osinbajo ya yi kira ga yan Najeriya dake ciki da wajen Najeriya su cigaba da kasancewa tsintsiya ɗaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel