Tsohon Jigon APC yace ‘Yan Najeriya su shiryawa bakar wahala bayan ganin kasafin 2022

Tsohon Jigon APC yace ‘Yan Najeriya su shiryawa bakar wahala bayan ganin kasafin 2022

  • Timi Frank yana ganin kasafin kudin 2022 ba zai kawo wa talaka wani sauki ba
  • ‘Dan siyasar yace za a gamu da karin haraji duk da mutane suna cikin fatara
  • Kwamred Frank ya yi hasashen za a kara kudin man fetur da wutar lantarki

Abuja - Tsohon mataimakin sakataren yada labarai na jam’iyyar APC na kasa, Timi Frank, ya yi kira ga al’ummar Najeriya su shirya fuskantar kalubale.

This Day ta rahoto Kwamred Timi Frank yana wannan jawabin a matsayin martani ga kasafin kudin shekarar 2022 da shugaban Najeriya ya gabatar.

Timi Frank yace abin da yake shiga aljihunan mutane ya ragu, sannan fetur da wuta za su kara tsada, baya ga wasu haraji da gwamnati za ta shigo da su.

A wani jawabi da ya fitar a birnin tarayya Abuja a ranar Lahadi, Frank yace a shirya shan wahala domin kasafin kudin badi ba zai kawo wa al’umma sauki ba.

Kara karanta wannan

Buhari ya yi alkawari Gwamnatinsa za ta kammala ayyukan da ta fara kafin ya bar mulki

'Dan adawar ya lissafo irin harajin da ke kan 'dan Najeriya, yace za a iya shigo da wasu a 2022.

Shugaba Buhari
Shugaba Buhari da Malam El-Rufai Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Facebook

Jawabin Timi Frank

“Buhari ya fada cewa gwamnatinsa tana harin N17.70tr a matsayin kudin shiga a 2022. Duk da haka akwai gibin N6.26tr, ya kara bashin da ke kan Najeriya.”
“Hakan ya na iya nufin cewa za a shigo da wasu sababbin haraji, ko a kara abin da ake karba.” - Timi Frank

Frank yace a shekarar 2021 gwamnati ta kara harajin VAT daga 5% zuwa 7.5%, sannan ana cire N50 da zarar mutum ya tura kudin da suka kai N1 000 a banki.

Tsohon kakakin na APC yace an dawo da tsarin shingogi da manyan hanyoyi, wanda hakan zai sa masu tuka mota su fara biyan harajin N200, N500 ko N1000.

Kara karanta wannan

2023: Jigon APC da ya shiga gidan yari ya fito, yana maganar neman Shugaban kasa

Da yake jawabi, Frank ya yi kaca-kaca da ‘yan majalisa a kan gaggawan da suka yi wajen amince wa da kudirin PIA, yace ba saboda talaka aka shigo da dokar ba.

“’Yan amshin shatan majalisar tarayya sun yi wuf sun amince da kudirin PIA, ba don kishin-kasa ba, sai saboda Buhari su cigaba da iko da kadarorin kasa.” - Timi Frank

Dazu kun ji a kasafin da aka yi na 2022, abin da za a kashe na sayen motoci ya kai Naira biliyan 1.6. Wannan kudi za su tafi ne wajen sake motocin da Aso Vila.

Hakan na zuwa ne bayan an ji za a batar da Naira miliyan 30 wajen sayen man fetur a fadar shugaban kasan, sannan shugaban kasa zai ci abincin N640m.

Asali: Legit.ng

Online view pixel