'Na warke Sarai', Tinubu ya mika godiya ga wadanda suka masa addu'a
- Gogaggen dan siyassa, Bola Asiwaju Tinubu ya dawo Najeriya bayan jinyar watanni uku da ya yi a London
- Asiwaju ya ce ya warke sarai kuma ya dawo domin ya dasa assasa damokaradiyya tare da shugabanci nagari a kasar
- Jigon APC, ya yi godiya ga Buhari, 'yan majalisa, gwamnoni da duk wadanda suka kai masa ziyara ko kiransa a waya
Asiwaju Bola Tinubu, jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ya ce ya warware sarai daga jinyar da yayi.
Daily Trust ta ruwaito yadda Tinubu ya kwashe watanni uku a London ya na jinya. An yi masa aiki ne a guiwa kuma zamansa ya sa manyan 'yan siyasa suka dinga zarya zuwa London.
A wata takarda da ofishin yada labaransa ya fitar a madadinsa a ranar Juma'a, Tinubu ya ce ya dawo kuma ya "warke sarai sannan zai cigaba da ayyukansa na bunkasa damokaradiyya da mulki na gari a kasar sa."
"Aiswaju Bola Tinubu ya dawo kasarsa inda ya sauka a jihar Legas a yammacin Juma'a a ranar 8 ga watan Oktoba. Ya iso daga London, UK.
"A tafiyar da ya yi, an yi masa aiki a guiwarsa ta dama kuma daga bisani ya zauna aka dinga duba kashin guiwar.
"Akasin rade-radin da ya dinga yawo, babu wani aiki bayan wannan da aka yi masa kuma ko a nan gaba ba za a sake ba. Ya samu sauki babu wata damuwa.
“Ya dawo gida lafiya kuma cike da lafiya. Asiwaju da farko ya na mika godiyarsa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan yadda ya dauka lokacinsa har ya ziyarcesa a London tare da yi masa fatan waraka.
"Ya mika godiyarsa ga kakakin majalisar wakila, Femi Gbajabiamila, gwamoni, shugabannin jam'iyya, 'yan majalisar wakilan arewa, 'yan majalisar jihar Legad sa sauran wadanda suka kira ko kai masa ziyara a London."
Gbajabiamila da 'yan siyasa 58 da suka kashe miliyoyi wurin ziyartar Tinubu
A wani labari na daban, a kalla jiga-jigan 'yan siyasa 58 tare da wadanda ke rike da ofisoshin siyasa a kasar nan suka kashe miliyoyin naira wurin kai wa jigon jam'iyyar APC, Asiwaju Boka Tinubu ziyara a London, Daily Trust ta ruwaito.
Tinubu jigon jam'iyya mai mulki ne wanda ya kwashe watanni uku a London ya na jinya. Makusancin tsohon gwamnan jihar Legas ya ce an yi masa aiki a guiwa kuma a halin yanzu likitocin kashi ne ke kula da shi.
Tun ranar 12 ga watan Augusta, yayin da shugaban kasa Muhammadu Burai ya ziyarcesa a London, yaransa na siyasa, masoyansa da magoya bayansu suka mayar da gidan tamkar filin arfa.
Asali: Legit.ng