Fasto ya ce ubangijinsa ya ba shi sako ya ba Buhari kan a daina siyo jiragen yaki
- A wani sabon zubin, Fasto Mbaka ya sake caccakar shugaba Buhari, inda ya ce ya bashi sakon ubangiji
- Mbaka ya nemi shugaba Buhari da ya daina sayen jiragen yaki ya dukufa wajen gina masana'antu
- Ya bayyana haka ne jim kadan bayan gwamnatin Buhari ta karbi karin kayan aikin yaki da 'yan ta'adda
Enugu - Shahararren malamin addinin kirista na Adoration Ministry da ke jihar Enugu, Rev. Fr. Ejike Mbaka, ya caccaki shugaban kasa Muhammadu Buhari kan cewa, ya daina siyan jiragen yaki ya dukufa wajen gina karin masana’antu.
A cewar malamin na addinin kirista, sakon da ya fada wa Buhari daga ubangiji ne, PM News ta ruwaito.
Ya shaida wa shugaban cewa jiragen da yake sayowa za a yi amfani da su ne wajen lalata kasar.
Da duminsa: 'Yan daba sun yi wa babban jami'in APC duka har ya gigice, sun kona gidansa a jihar Nasarawa
Mbaka ya bayyana hakan ne a lokacin da yake wa’azi a cocin sa ranar Lahadi 10 ga watan Oktoba.
A kalamansa:
“Jiragen da kake saya za a yi amfani da su don durkusar da Najeriya.
“Don Allah, duk mutumin da ya fara saduwa da Shugaba Buhari bayan wannan sakon, ya gaya masa cewa duk wadannan jiragen da yake sayowa za a yi amfani da su don lalata Najeriya.
"Ubangiji ya ce in gaya masa haka."
"Ya kamata ya daina siyan karin jiragen sama na yaki ya kuma fara gina karin masana'antu."
Buhari, yayin da yake magana a makon da ya gabata, ya tabbatar da cewa gwamnatinsa ta karbi karin kayayyakin aiki a ci gaba da ake da yaki da abokan gaba na kusa da na nesa.
A cewar Buhari:
"Za a tura wadannan kayan aikin don hanzarta yaki da rashin tsaro a dukkan sassan kasar."
Kashi na biyu na jiragen yakin A-29 Super Tucano sun nufo Najeriya
Kashi na biyu na jiragen yaki guda 6 kirar 'A-29 Super Tucano' sun baro ƙasar Amurka, sun kamo hanyar zuwa Najeriya.
Mai taimakawa shugaban kasa ta ɓangaren yada labarai, Tolu Ogunlesi, shine ya bayyana haka a shafinsa na Facebook.
A wani rubuta da ya tura a shafinsa daga Telegram, Ogunlesi ya bayyana cewa jiragen yakin sun tsaya a Rectrix domin zuba musu mai zuwa Najeriya.
Ya kamata 'yan Najeriya su fahimci ilimin Buhari don gane tasirinsa, Minista
A bangare guda, Ministan Ayyuka da Gidaje na Najeriya, Babatunde Fashola, ya ce dole ne 'yan Najeriya su san ilimi da horon da shugaban kasa Muhammadu ya samu don fahimtar tasirin sa kan mulki.
Ministan ya bayyana hakan ne a cikin shiri mai taken, 'The Effect Buhari: Undeniable Achievements', wanda aka watsa a gidan Talabijin na Channels a yammacin Asabar 9 ga watan Oktoba.
Shirin na awa daya ya ba da labarin wasu “nasarori” na gwamnatin Buhari a duk fannonin shugabanci da suka hada da ci gaban ababen more rayuwa, gidaje, noma, sufuri, kiwon lafiya, da sauran su.
Asali: Legit.ng