Tsagerun yan bindiga sun yi awon gaba da shugaban matasa, Sun nemi a tattaro miliyoyi kudin fansa

Tsagerun yan bindiga sun yi awon gaba da shugaban matasa, Sun nemi a tattaro miliyoyi kudin fansa

  • Miyagun yan bindiga sun yi awon gaba da shugaban ƙungiyar matasa NYCN a kan hanyarsa ta zuwa Ogun
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa masu garkuwan sun tuntuɓi iyalan gidan mutumin, sun nemi a tattaro miliyan N30m
  • Kakakin yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, yace a halin yanzun jami'ai na cigaba da ƙoƙarin ceto shi

Ogun - Yan bindiga sun sace Olamilekan Okunuga, shugaban ƙungiyar matasa (NYCN), reshen ƙaramar hukumar Odogbolu jihar Ogun.

Premium times ta rahoto cewa maharan sun yi awon gaba da mista Okunuga a kan hanyar Ogere jihar Ogun, akan hanyarsa bayan ya baro Ibadan ranar Alhamis.

Rahotanni sun bayyana cewa an bar motar shugaban matasan a kan hanya, bayan tsagerun sun tasa ƙeyarsa.

Read also

Halin da yan bindiga suka jefa mutane tun bayan katse hanyoyin sadarwa a jihar Katsina

Yan bindiga
Tsagerun yan bindiga sun yi awon gaba da shugaban matasa, Sun nemi a tattaro miliyoyi kudin fansa Hoto: guardian.ng
Source: UGC

Yan fashin sun nemi a biya kuɗin fansa

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, shugaban NYCN na jihar Ogun, Abduljabar Ayelaagbe, yace masu garkuwan sun bukaci a biya miliyan N30m.

Ayelaagbe ya ƙara da cewa an gano motar wanda aka sace ɗin a hannun wani mutumi da ba'a san shi ba, wanda ya tuƙa ta zuwa Ogijo.

Yace:

"Shugaban ƙungiyarmu reshen ƙaramar hukumar Odogbolu ya faɗa hannun masu garkuwa da mutane kwana biyu zuwa uku nan baya a yankin Ogere, jihar Ogun."
"Yaje Ibadan ne, akan hanyarsa ta dawowa ne yan bindiga suka sace shi. Tun a daren da aka sace shi muka gano an watsar da motarsa a kan hanya."
"An faɗa mana cewa masu garkuwan sun nemi iyalansa su tattara musu miliyan N30m a matsayin kuɗin fansa."

Read also

Wata Sabuwa: Jami'an Kwastam sun sake bude wuta kan jama'a a jihar Katsina

Wane mataki yan sanda suka ɗauka?

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da lamarin, yace mutumin da aka gano ya tuka motarsa yana hannun su.

Ya kuma bayyana cewa a halin yanzun lamarin na cikin bincike yayin da jami'an yan sanda ke kokarin ceto shugaban matasan, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

A wani labarin na daban kuma Yan sakai sun hallaka limamin masallaci da wasu mutum 10 a jihar Sokoto

Rahotanni sun bayyana cewa an kashe mutanen ne baki ɗayansu a kasuwa, yayin da wasu huɗu suka jikkata.

Wani ɗan uwan limamin da aka kashe, yace ba abinda ɗan uwansa ya yi sai kawai dan yakasance Bafullatani.

Source: Legit

Online view pixel