An yi taron murnar dawowar Tinubu Najeriya, ya magantu kan tafiya da dawowarsa

An yi taron murnar dawowar Tinubu Najeriya, ya magantu kan tafiya da dawowarsa

  • Bola Tinubu ya dawo Najeriya bayan shafe watanni a kasar Landan saboda rashin lafiyar da yayi
  • Ya mika godiyarsa ga Allah bisa dawowarsa gida Najeriya bayan shafe watanni a kasar waje
  • An yi taron dawowarsa Najeriya a gidan gwamnatin jihar Legas, inda manyan siyasa suka halarta

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, jagoran jam’iyyar APC na kasa Bola Tinubu ya mika godiya ga Allah da ya dawo da shi Najeriya lafiya.

Ya yi magana ne a gidan gwamnati da ke Marina a wani taro don maraba da dawowarsa gida.

Tinubu ya fita zuwa kasar waje cikin watanni uku da suka gabata inda aka yi masa tiyata a gwiwa.

Da dumi-dumi: An yi taron murnar dawowar Tinubu Najeriya, ya magantu kan tafiyarsa
Tinubu ya dawo Najeriya | Hoto: dailytust.com
Asali: Facebook

Wadanda suka hallara a wurin taron akwai uwargidan Gwamnan jihar Legas Misis Ibijoke Sanwo-Olu, Mataimakin Gwamna Obafemi Hamzat; matarsa Oluremi da tsohuwar Mataimakiyar Gwamnan Legas Misis Idiat Adebule.

Kara karanta wannan

‘Yan siyasan Arewa 10 da ke kan gaba wajen neman kujerar shugaban Jam’iyyar PDP

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakazalika da Kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila; Kakakin majalisar jihar Legas Mudashiru Obasa; Sanata Olamilekan Solomon, da sauran su.

Jagoran APC Bola Tinubu ya dawo Najeriya bayan jinya a Landan

Jagoran jam'iyyar APC, Bola Tinubu, ya dawo gida Najeriya bayan yi masa tiyata a birnin Landan na ƙasar Birtaniya.

The Cable ta rahoto cewa Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas, ya dawo Najeriya ne ranar Jumu'a da yamma.

A wata sanarwa da kakakinsa, Tunde Rahman, ya fitar, ya bayyana cewa an yiwa tsohon gwamnan tiyata a guiwarsa ta dama.

Gwamna ya je Landan dubo Bola Tinubu, ya gano dalilin makalewarsa a kasar waje

A wani labarin, Gwamna Kayode Fayemi ya musanta ikirarin cewa ya tafi Ingila kwanan nan don ziyartar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu kan batun zaben 2023, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Wata jami'a ta sanya wa tsangaya sunan shahararriyar mawakiya Magajiya Danbatta

Gwamnan na Ekiti wanda ya zanta da manema labarai a ranar Lahadi, 26 ga watan Satumba, ya ce ya ziyarci Tinubu ne saboda an yi masa tiyata kwanan nan, ya kara da cewa ba shi da alaka da tsare-tsaren zaben 2023 da ake zargi.

Fayemi ya ce a matsayinsa na dattijo kuma jigo na jam’iyyar APC, Tinubu ya cancanci a nuna masa kauna da kulawa a lokutan bukata wanda shine babban dalilin da yasa ya kai masa ziyara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel