Lai Mohammed: Babu dama-dama tsakanin 'yan bindiga da 'yan awaren IPOB

Lai Mohammed: Babu dama-dama tsakanin 'yan bindiga da 'yan awaren IPOB

  • Ministan Buhari ya bayyana cewa, gwamnatin Buhari ba ta nuna banbanci tsakanin 'yan ta'adda
  • A cewarsa, 'yan IPOB da 'yan bindiga duk daya suke, kuma hanya daya ake bi wajen dakile su
  • Ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa a wata hira da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN)

Ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed, ya ce babu wani fifiko da ake nunawa tsakanin 'yan bindiga, masu tayar da kayar baya da kuma 'yan aware, The Cable ta ruwaito.

Mohammed yana mayar da martani ne kan zargin da ake yi na cewa gwamnatin tarayya tana ririta 'yan bindiga amma kuma ba ta daga wa 'yan IPOB da sauran 'yan aware kafa.

Da yake zantawa da NAN, ministan ya bayyana zargin a matsayin rashin fahimta kuma labaran bogi da aka cakuda waje daya.

Read also

Fasto ya ce ubangijinsa ya ba shi sako ya ba Buhari kan a daina siyo jiragen yaki

Lai Mohammed: Babu dama-dama tsakanin 'yan bindiga da 'yan aware
Minsitan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed | Hoto: dailynigerian.com
Source: UGC

Ya kuma bayyana cewa, batu ya je ga gwamnati cewa, an samu wasu da ke yada bayanan cewa, sojoji na ragargazar 'yan IPOB amma suna sanya ga 'yan bindiga.

A cewarsa, gwamnati ba ta banbance 'yan ta'adda, kuma duk dan ta'adda sunansa dan ta'adda.

Da yake Allah wadai da batun da ake yadawa, Mohammed ya ce:

"Ina so in fadi ba tare da wani jinkiri ba cewa wannan kuskure ne. Ba gaskiya ba ne, ba daidai ba ne kuma labaran karya ne aka cakuda waje daya.
“Maganar gaskiya ita ce, gwamnatin tarayya ba ta banbance tsakanin 'yan ta’adda da ‘yan fashi. A idon gwamnatin tarayya dukkan su masu laifi ne kuma ana bi dasu ta hanya daya.
“Yana da matukar muhimmanci a daidaita batun. Me yasa na fadi haka? Domin, ci gaba ne na maganganun barna na wasu masu sharhi.”

Read also

Hawan farashi: Ana hasashen tsadar iskar gas zai kai N10k a 12.5 nan gaba kadan

Ministan ya ce bai kamata a sanya siyasa kan batun tsaro ba.

A kalamansa cewa yayi:

“Batun tsaro bai kamata a siyasantar da shi ba. Tsaro tsaro ne. 'Yan bindiga suna kashe sojoji; suna kashe ‘yan sanda da mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

"Don haka, me yasa sojoji za su yi wasa akan wani bangaren 'yan ta'adda kan wani?"

An tattauna da 'yan bindiga a Zamfara, sun sako mutane sama da 200

Gwamnatin jihar Zamfara a ranar Alhamis ta ce ta tabbatar da sakin akalla mutane 200 da ‘yan bindiga suka sace ta hanyar tattaunawa ta lumana da sauran matakan tsaro.

Mukaddashin Gwamnan Zamfara, Nasiru Magarya, ya bayyana hakan lokacin da ya karbi bakuncin Taron Shugabannin Majalisar Dokokin Jihohin Najeriya, a Gusau.

Mista Magarya, wanda shine kakakin majalisar dokokin Zamfara, ya tarbi tawagar, wacce ta kai masa ziyarar jaje bisa rasuwar mahaifinsa, Mu’azu Magarya, Daily Nigerian ta ruwaito.

Read also

Gwamnatin tarayya ta kara kudin wutan lantarki ba tare da sanar da yan Najeriya ba, Bincike

A baya mun kawo muku rahoton cewa, Mahaifin mai kakakin majalisar ya mutu yayin da yake hannun 'yan bindiga.

Tawagar, a karkashin jagorancin Shugaban Taron kuma Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, Abubakar Sulaiman, ta kuma kunshi shugabannin majalisar Kano, Katsina da Yobe.

Mista Magarya ya yabawa musu bisa ziyarar, ya kara da cewa kalubalen tsaro da ke damun Zamfara ya zama abin damuwa ga gwamnatin da Gwamna Bello Matawalle ke jagoranta.

Ya kuma, ya tabbatarwa da maziyarta da mutanen jihar kudirin gwamnati na magance matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Ya kamata 'yan Najeriya su fahimci ilimin Buhari don gane tasirinsa, Minista

A wani labarin, Ministan Ayyuka da Gidaje na Najeriya, Babatunde Fashola, ya ce dole ne 'yan Najeriya su san ilimi da horon da shugaban kasa Muhammadu ya samu don fahimtar tasirin sa kan mulki.

Read also

Na fi zama cikin nishadi da farin ciki yayin da nake cikin fatara, Mawaki Akon

Ministan ya bayyana hakan ne a cikin shiri mai taken, 'The Effect Buhari: Undeniable Achievements', wanda aka watsa a gidan Talabijin na Channels a yammacin Asabar 9 ga watan Oktoba.

Shirin na awa daya ya ba da labarin wasu “nasarori” na gwamnatin Buhari a duk fannonin shugabanci da suka hada da ci gaban ababen more rayuwa, gidaje, noma, sufuri, kiwon lafiya, da sauran su.

Source: Legit

Online view pixel