Ban taba ganin Shugaban kasa mai hakuri irin Shugaba Muhammadu Buhari ba, Lai Mohammed

Ban taba ganin Shugaban kasa mai hakuri irin Shugaba Muhammadu Buhari ba, Lai Mohammed

  • Alhaji Lai Mohammed ya bayyana irin hakurin da shugaba Buhari ke da shi
  • A cewarsa, bai taba ganin mutum mai hakuri irin shugaba Buhari
  • Lai ya tabbatar da cewa akwai Ministocin da shirme kawai suke fada a taron FEC

Abuja - Ministan Labarai da al'adu, Lai Mohammed, ya bayyana cewa shi dai har yanzu bai taba ganin wani Shugaba mai hakuri irin shugaba Muhammadu Buhari.

Ministan wanda yayi magana ranar Juma'a yayinda ya karbi bakuncin tawagar wakilan gammayar kasashen Afrika (AUDA-NEPAD) da (APRM), rahoton TheCable.

Lai Mohammed yace dubi ga irin dimbin kalubalen da Najeriya ke fama cikin shekaru shida da suka gabata, ana bukatar hakuri da azanci.

Yace:

"Jagoranta kasa irin Najeriya kamar wata karamar duniya ce kuma shi yasa nike girmama hakuri, azanci da salon shugabancin shugaban kasa."

Read also

Ya kamata 'yan Najeriya su fahimci ilimin Buhari don gane tasirinsa, Minista

"Abinda yasa na fadi haka shine cikin shekar shida da suka gabata, ina halartan taron majalisar zartaswa."
"Akan ko wani lamari, shugaban kasa na sauraron dukkan Ministoci 43 inda suna son tsokaci."
"Duk da cewa mun san shirme wasu ke fada cikin Ministocin, shugaban kasa zai sauraresu kuma yace 'Nagoda' a karshe."

Ministan ya kara da cewa "har yanzu ban ga shugaba mai hakuri da fahimta irin Shugaba Muhammadu Buhari ba."

Ban taba ganin Shugaban kasa mai hakuri irin Shugaba Muhammadu Buhari ba, Lai Mohammed
Ban taba ganin Shugaban kasa mai hakuri irin Shugaba Muhammadu Buhari ba, Lai Mohammed
Source: Facebook

Shugaba Buhari ya dira jihar Kaduna don halartan bikin yaye daliban makarantar Soji NDA

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya dira jihar Kaduna ranar Juma'a domin halartan bikin yaye daliban jami'ar horar da Sojojin Najeriya, NDA, da aka shirya ranar Asabar, 9 ga Oktoba, 2021.

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook da yammacin Juma'a.

Read also

Wata sabuwa: Buhari na shirin tsige Atoni-Janar Malami da wasu ministoci 14

A riwayar Leadership, Jirgin Shugaban kasan ya dira barikin Sojin sama dake Mando Kaduna ne daidai karfe 4:40.

Shugaban kasa ya samu rakiyar Ministan tsaro, Bashir Salihi Magashi, dss.

Source: Legit

Online view pixel