Hotunan kyakyawar budurwar da ta rasu ana saura kwanaki 3 auren ta

Hotunan kyakyawar budurwar da ta rasu ana saura kwanaki 3 auren ta

  • Kyawawan hotuna tare da katin gayyatar daurin auren Wasilat Attahir, budurwar da ta rasu ana sauran kwana 3 auren ta sun bayyana
  • Cike da alhini tare da tashin hankali kawar amaryar ta wallafa inda ta ke bada labarin yadda suka yi bayan ta kai mata gayyatar
  • Kamar yadda katin ya bayyana, za a daura auren a garin Dutsin-Ma a jihar Katsina ranar Asabar, 9 ga watan Oktoba mai zuwa

Dutsin-Ma, Katsina - Wata matashiyar budurwar Najeriya mai suna Wasilat Attahir, ta amsa kiran mahaliccin ta ana sauran kwanaki uku daurin auren ta.

An tattaro cewa, an shirya tsaf za a daura auren Wasilat a ranar Asabar mai zuwa, 9 ga watan Oktoba a garin Dutsin-Ma da ke jihar Katsina.

Read also

Sarkin Musulmi Da Shugaban CAN Sun Buƙaci a Kama Musulmin Da Suka Kashe Fasto a Kano

Wata kawar marigayiyar mai suna Xahreert Uthman Faruq ta wallafa katin gayyatar daurin auren wasilat a shafin ta na Facebook tare da bayyana yadda suka yi.

Hotunan kyakyawar budurwar da ta rasu ana saura kwanaki 3 auren ta
Hotunan kyakyawar budurwar da ta rasu ana saura kwanaki 3 auren ta. Hoto daga Mhiz Xahreert Uthman Faruq
Source: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hotunan kyakyawar budurwar da ta rasu ana saura kwanaki 3 auren ta
Hotunan kyakyawar budurwar da ta rasu ana saura kwanaki 3 auren ta. Hoto daga Mhiz Xahreert Uthman Faruq
Source: Facebook

Hotunan kyakyawar budurwar da ta rasu ana saura kwanaki 3 auren ta
Hotunan kyakyawar budurwar da ta rasu ana saura kwanaki 3 auren ta. Hoto daga Mhiz Xahreert Uthman Faruq
Source: Facebook

Benue: 'Yan bindiga sun halaka rayuka 2 a sabon farmaki

A wani labari na daban, Miyagun 'yan bindiga sun halaka rayuka biyu a yankin Nyiev da ke karamar hukumar Guma ta jihar Benue.

Lamarin ya faru ne kusan kwana biyu bayan da aka kashe rayuka tara a wurare daban-daban na karamar hukumar, Daily Trust ta wallafa.

Shugaban karamar hukumar Guma ta jihar Benue, Caleb Aba, ya sanar da Daily Trust cewa, a ranar Alhamis 'yan bindigan suka zagaye yankin Nyiev kuma suka bude wa mazauna yankin wuta.

Source: Legit.ng

Online view pixel