Babban jigon APC a arewa ya gaya wa Buhari Minista na gaba da za a sauke daga aiki

Babban jigon APC a arewa ya gaya wa Buhari Minista na gaba da za a sauke daga aiki

  • An yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya sallami karin ministoci wadanda ba sa amfani da ofisoshinsu don inganta rayuwar 'yan Najeriya
  • Wani jigo a jam’iyyar APC daga jihar Kano, Abdulmajid Danbilki Kwammanda, ya bukaci Shugaba Buhari da ya kori Ministan Tsaro, Bashir Magashi
  • Kwammanda yayi ikirarin cewa yanayin tsaro a Najeriya ya bayyana karara cewa Magashi baya yin aikinsa

A tsaka da sauye-sauyen majalisar ministocin shugaba Buhari, an yi kira da a kori wasu ministocin masu ci wadanda ake zargin ba su aikin kwarai.

Daya daga cikin irin wannan ministoci da aka sako a gaba shine Ministan Tsaro, Bashir Magashi.

Babban jigon APC a arewa ya gaya wa Buhari Minista na gaba da za a sauke daga aiki
Babban jigon APC a arewa ya gaya wa Buhari Minista na gaba da za a sauke daga aiki Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

A jawabinsa a ranar Juma’a, 3 ga watan Satumba, Abdulmajid Danbilki Kwammanda, wani jigo a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Kano, ya bayar da hujjar cewa bai taba samun kwarin gwiwa kan ikon Magashi na yin aiki a ma’aikatar ba tun bayan nadinsa, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Usman Baba Alkali: Na zama IGP a lokacin da a ke tsaka da fuskantar jarabawa

Kwammanda wanda ya danganta matsayinsa kan karuwar rashin tsaro a yankin arewacin kasar, ya ce akwai kwararan hannaye a Kano wadanda za su iya yin aikin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Don haka, ya yi kira ga Shugaba Buhari da ya kori ministan sanna ya maye gurbinsa da wanda ya fi shi cancanta, jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Kalamansa:

“Kirana ga Shugaban kasa shi ne ya kori ministan tsaro. Idan kuka kalli yanayin tsaro a Najeriya, musamman a Arewa, za ku yarda da ni cewa Ministan baya yin aikinsa.
"Buhari yana iya bakin kokarinsa don kamo kalubalen tsaro amma a matsayinsa na Minista, Magashi baya yin komai. Don haka, ina kira ga Buhari da ya gaggauta sauke shi daga mukaminsa, ya maye gurbinsa da wanda ya fi shi cancanta.
"Muna da kwararrun mutane daga jihar Kano don maye gurbin Nanono da Magashi."

Kara karanta wannan

Kungiya ta yi kira ga Buhari ya tsige wasu Ministoci 2 da Hadiminsa bayan su Sabo Nanono

Abubuwa 2 da Shugaban kasa ya duba kafin ya yi waje da Sabo Nanono da Saleh Mamman daga ofis

A wani labari, a ranar Alhamis, 2 ga watan Satumba, 2021, Fadar Shugaban kasa ta yi karin haske a kan abin da ya sa Muhammadu Buhari ya kori Ministoci.

Punch tace hadimin shugaban kasar Najeriya, Femi Adesina ya yi wannan bayani a lokacin da aka yi hira da shi a gidan talabijin a ranar Alhamis.

Mai taimaka wa shugaban kasar wajen yada labarai da hulda da jama’a, Femi Adesina yace Buhari yayi la’akari da batun abinci da sha’anin lantarki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel