Rikici ya sake ballewa tsakanin yan Boko Haram da yan ISWAP, an kashe mutum 85

Rikici ya sake ballewa tsakanin yan Boko Haram da yan ISWAP, an kashe mutum 85

  • Yan ta'addan ISWAP sun kai harin ramuwar gayya kan yan Boko Haram
  • Wannan na zuwa ne kwanaki biyar bayan da yan Boko Haram suka kai musu hari
  • Tun bayan mutuwa Shekau ake batakashi tsakanin kungiyoyin ta'addan biyu

Kwanaki biyar bayan harin da yan ta'addan Boko Haram suka kaiwa yan ta'addan ISWAP inda suka hallaka mutum 24 cikin, yan ta'adda sun sake karkashe juna.

A farkon makon nan yan Boko Haram sun kai hari tsaunin Mandra da Gaba dake garin Gwoza a jihar Borno.

Rahoton leken asiri ya nuna cewa rikicin ya barke ne ranar Talata.

A cewar PRNigeria, yan ISWAP sun kai harin ramuwar gayya ne sansanin Kwamandan Boko Haram, Bakoura Modou, a yankin tafkin Chadi.

Rahoton ya kara cewa ISWAP ta sake rashin mayaka 87.

Kara karanta wannan

Jami’an DSS sun kama Hadimin Gwamna, mutum 2 da zargin satar kudin da aka ware wa talakawa

Wata majiya tace:

"Sama da yan ta'addan ISWAP 87 aka kashe a harin."

Rikici ya sake ballewa tsakanin yan Boko Haram da yan ISWAP, an kashe mutum 85
Rikici ya sake ballewa tsakanin yan Boko Haram da yan ISWAP, an kashe mutum 85
Asali: UGC

Borno: An tafka ƙazamin faɗa tsakanin Boko Haram da ISWAP, an kashe 24

Yan ta'addan Boko Haram sun kashe mayakan Islamic State of West Africa Province, ISWAP guda 24 a duwatsun Mandra da Gaba a yankin Gwoza a ranar Juma'a.

Lamarin ya faru ne a yayin da yan Boko Haram din karkashin wani kwamanda Aliyu Ngulde, suka yi musayar wuta da mayakan ISWAP karkashin jagoracin wani Abou Aseeya a yankin mai duwatsu.

Yayin rikicin tsakanin kungiyoyin masu gaba da juna an kama yan ISWAP da dama da ransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng