Borno: An tafka ƙazamin faɗa tsakanin Boko Haram da ISWAP, an kashe 24

Borno: An tafka ƙazamin faɗa tsakanin Boko Haram da ISWAP, an kashe 24

  • Yan ta'addan Boko Haram sun hallaka yan ISWAP guda 24 a Gwoza a ranar Juma'a
  • Sun kashe su ne sakamakon musayar wuta da kungiyoyin biyu suka yi a duwatsun Mandara da Gaba
  • Yayin fadar tsakanin su kungiyoyin biyu masu gaba da juna, an kama yan ISWAP da dama da ransu

Borno - 'Yan ta'addan Boko Haram sun kashe mayakan Islamic State of West Africa Province, ISWAP guda 24 a duwatsun Mandra da Gaba a yankin Gwoza a ranar Juma'a.

Lamarin ya faru ne a yayin da yan Boko Haram din karkashin wani kwamanda Aliyu Ngulde, suka yi musayar wuta da mayakan ISWAP karkashin jagoracin wani Abou Aseeya a yankin mai duwatsu.

Borno: An tafka ƙazamin faɗa tsakanin Boko Haram da ISWAP, an kashe 24
An tafka ƙazamin faɗa tsakanin Boko Haram da ISWAP, an kashe 24 a Borno. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kame waɗanda ake zargi da kisan babban malamin Addini a jihar Kano

Yayin rikicin tsakanin kungiyoyin masu gaba da juna an kama yan ISWAP da dama da ransu.

A cewar wasu majiyoyi da suka yi magana da PRNigeria, rikicin tsakanin kungiyoyin biyu na ramuwayar gayya ne sakamakon harin da 'yan ISWAP suka rika kai wa yan Boko Haram a baya-bayan nan.

Sojojin Nigeria su dakile harin da 'yan ISWAP suka kai sansanin 'yan Boko Haram

Kazalika, dakarun sojojin Nigeria sun dakile wani harin da 'yan ISWAP suka yi niyyar kai wa sansanin tubabbun yan Boko Haram da ke karamar hukumar Damboa a jihar Borno.

Sojojin sun dakile harin da yan ta'ddan da suka kutsa garin da motocci masu dauke da bindiga suka kai.

Sahihan majiyoyi sun tabbatarwa PRNigeria sun tabbatar da cewa mayakan ISWAP sun kai harin a ranar Asabar da yamma a garin.

Ya ce:

"Sansanin ne inda aka ajiye tubabbun yan Boko Haram tun bayan da suka mika wuya suka tuba."

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane 2 su na tsaka da amsar kuɗin fansa

Amma ya ce cikin gaggawa an tura dakarun sojoji wurin sun kuma fatattaki yan ta'addan.

Wani jami'in soja na sashin binciken sirri ya ce:

"Duk da an dakile harin yan ta'addan bayan musayar wuta, ba zan iya tabbatar da adadin wadanda suka mutu ba."

Hotunan Mutane 5 Masu Garkuwa Da Mutane Da Ƙwararrun Mafarauta Suka Kama a Kogi

A wani labarin daban, kwararrun mafarauta a karamar hukumar Okehi a jihar Kogi sun yi nasarar kama mutane biyar 'yan kungiyar masu garkuwa da mutane, LIB ta ruwaito.

An kama mutane biyar din da ake zargi a safiyar ranar Talata a Atami, wani gari da ke wajen Osara a ranar Talata, 27 ga watan Satumban shekarar 2021.

King Habib, babban hadimi ga shugaban karamar hukumar Okehi a bangaren watsa labarai, Hon Abdulraheem Ohiare Ozovehe ya tabbatar da kama wadanda ake zargin, yana mai cewa tawagar sun dade suna adabar mutane a titin Okene-Lokoja da Okene-Auchi a jihar Kogi State.

Kara karanta wannan

'Yan fashi sun afka wa coci domin sace kudi, sun daba wa mai gadi wuka a Abuja

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel