Cikakken Bayani: Yadda Kotu ta wanke Sheikh Zakzaky da matarsa, ta umarci a sake su
- A yau dai an yanke hukunci kan Sheikh Zakzaky, kuma an wanke shi dashi da matarsa
- Kotu ta ba da umarnin a saki Sheikh Zakzaky bayan da ta tabbatar da bashi da wani laifi
- Wani lauya ya yi tsokacin dalilin da yasa kotu ta wanke malamin tare da matarsa Zeenatu
Rahotanni da muke samu sun bayyana cewa, a yau 28 ga watan Yuli, an yanke hukunci kan Zakzaky da matarsa, inda tuni aka wanke su daga zargi.
A cewar lauyan Zakzaky, Barista Sadau Garba, kotun ta wanke waɗanda ake zargin daga zargi takwas da gwamnatin Jihar Kaduna ta gabatar mata.
Rahoton ya ce tuni bayan yanke hukuncin aka zarce da Zakzaky zuwa gida nan take, kuma ba a tsaya sauraran 'yan jarida ba.
Tun farko, ba a 'yan jarida da sauran jama'a damar shiga zauren kotun ba.
A cewar rahotanni, mai shari'a Gideon Kurada ne ya jagoranci shair'ar cikin sirri.
A cewar gidan talabijin na Channels, zaman sauraran shari'ar ya shafe akalla sa'o'i takwas kafin cimma wanke malamin da matarsa, tare da ba da umarnin sakinsu.
Dalilin da yasa kotu ta wanke Sheikh Zakzaky da matarsa
A cewar wakilin BBC:
"Kotun ta sallame su ne saboda rashin ƙwakkwarar hujja."
A nasa bangaren, yayin da yake tsokaci kan hukuncin, Barista Sadau ya ce:
"Ta yaya za a zargi mutum da aikata laifi a 2015 sannan kuma a tuhume shi da dokar da aka samar a 2017"
An dage shari'ar Abduljabbar zuwa wasu makwanni masu zuwa
A wani labarin daban, an dage shari'ar Abduljabbar zuwa wasu makwanni masu zuwa Lauyar gwamnati ta bayyana dalilan da yasa ta roki a dage shariar zuwa wani lokaci in da take cewa:
"Mun saurari jawabansa, kuma bayanansa azarbabi ne. Mun nemi kotu ta dage shari'ar ne domin mu kawo tuhumar da muke yi masa.
"Ai caji ya kunshi dukkan wani bayani da muke bukata. Lauyan wanda ake kara ba shi ne zai fada mana yadda za mu tsara kararmu ba. Kuma muna rokon kotu ta ba mu 25 ga watan Agusta, 2021, domin a ci gaba da shari'a.
Bayan doguwar caccaka tsinke, Alkali ya gamsu da bayanai daga dukkan bagarori, ya kuma yanke hukunci, inda ya amince da dage shari'ar zuwa wani lokaci.
BBC ta ruwaito cewa, Alkali ya dage shari'ar har zuwa nan da makwanni uku, wato za a sake zama ranar 18 ga watan Agustan wannan shekara. Hakazalika, malamin zai ci gaba da zama a gidan gyaran hali. Dukkan bangarori sun gamsu.
Asali: Legit.ng