Gwamnan Neja ya dakatad da zaben sabon Sarkin Kontagoran kan zargin murdiya

Gwamnan Neja ya dakatad da zaben sabon Sarkin Kontagoran kan zargin murdiya

  • Gwamnatin jihar Neja tace a sake sabon lale wajen zaben sabon sarkin Kontagora
  • Da farko an yi zabe har an sanar da Barau Muazu wanda ya lashe, amma abin ya bar baya da kura
  • Wannan ya biyo bayan mutuwar Sarkin Sudan wanda ya kusa shekaru 50 kan mulkin

Minna, Neja - Gwamnan jihar Neja, Abubakar Bello, ya yi watsi da nadin sabon Sarkin Kontagora, bisa karar da wasu yan takara 46 suka shigar kan zargin murdiya da rufa-rufa da akayi a zaben.

Hakazalika gwamnan ya canza kwamishanan harkokin sarakunan gargajiya. Abdulmalim Sarkin-Daji, wanda ake zargi da murdiyan, rahoton Premium Times.

A ranar Lahadi, an sanar da babban dan kasuwa Mohammadu Barau-Mu’azu, matsayin sabon Sarkin Kontagora, bayan samun rinjaye a zaben da masu zaben Sarki biyar suka kada.

Amma daga sanarwar, sauran yan takara suka fara zanga-zanga inda suka zargi Kwamishana Sarkin-Daji da rufa-rufa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari za ta san matsayar bashin $4bn nan da kwana 7, kwamiti zai zauna

Sun ce ba'ayi daidato wajen zaben ba saboda Kwamishanan na da wanda yake so.

Mika Anache, wanda ya shigar da kara madadin sauran yan takara 46 yace basu yarda da zaben da aka gudanar ranar 19 ga Satumba ba.

Gwamna ya dakatad da zaben sabon Sarkin Kontagoran kan zargin murdiya
Gwamnan Neja ya dakatad da zaben sabon Sarkin Kontagoran kan zargin murdiya Hoto: Mary Noel-Berje
Asali: Twitter

Sakamakon wadannan kararraki, Sakataren gwamnatin jihar, Ahmad Matane, a ranar Talata zaben da aka gudanar ya bar baya da kura.

Yace:

"Saboda nuna cewa gwamnatin jihar ba tada son rai kan wannan zabe, gwamnan jihar ya baa umurnin sake gudanar da zabe."
"Saboda haka, an sauke kwamishanan kananan hukumomi da lamuran sarakunan gargajiya, Barr Abdulmalik Sarkin-Daji daga kujerarsa kuma an mayar da shi ma'aikatar cigaban matasa."

Ya kara da cewa an nada Emmanuel Umar, sabon kwamishanan kananan hukumomi da lamuran sarakunan gargajiya na wucin gadi.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya dakatar da shugabannin makarantar da ya yi karatu yayin da ya kai ziyarar bazata

Yarimomi 45 sun shiga jerin masu neman mulkin Sarkin Sudan na Kontagora

Akalla Yarimomi 45 kawo yanzu sun bayyana niyyar na ahwa karagar mulkin Sarkin Sudan na Kontagora.

Shugaban kwamitin zaben Sarki, Alhaji Shehu Galadima, ya bayyanawa manema labarai cewa mambobin kwamitinsa zasu tabbatar da cewa an yi zaben gaskiya da lumana.

Wani mamban dattawan masarautar, Manjo Janar Suleiman Saidu (mai ritaya) yace babu wanda zai samu fifiko wajen kwamitin zaben.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng